Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ba da tallafin kayan jin ƙai mai nauyin ton 50 ga Nijeriya don taimaka wa waɗanda suka yi asarar gidaje sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru kwanan nan.
An mika kayan agajin ga jami’an gwamnati na Nijeriya ga hukumar kula da agajin gaggawa (NEMA), ma’aikatar harkokin waje, da Ofishin mai ba da shawara kan tsaron ƙasa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
- Daga Bisani Dai Ta Tabbata Dubai Ta Ɗage Haramcin Biza Ga ‘Yan Nijeriya
- Kakakin Ma’aiktar Tsaron Sin Ya Gabatar Da Yadda Aka Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa Na Sojojin Sin Da Tanzaniya Da Mozambique
Jakadan UAE a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya miƙa wannan tallafi a madadin Shugaba Sheikh Mohamed Al Nahyan, inda ya jaddada aniyar UAE na tallafa wa ƙasashen da ke fuskantar iftila’i.
A martaninsa, Dr. Ahmed Dunoma, Sakatare Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, ya gode wa UAE a madadin Shugaba Bola Tinubu, yana mai haskaka alaƙa tsakanin kasashen biyu.
Babbar Daraktar NEMA, Zubaida Umar, ta kuma nuna godiya ga UAE, tana mai cewa tallafin zai taimaka wajen ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa al’ummomin da ambaliyar ta shafa wajen rage raɗaɗi.