Hukumar Gudanarwar Kamfanin ‘Amasis Broadcasting Services Ltd’ mallakin gidan talabijin din Tambarin Hausa ta nada Ibrahim Sani Shawai a matsayin sabon manajan gudanarwa na gidan talabijin din.
Wannan bayanin na kunshe ne cikin saanrwar da shugaban majalisar koli kuma mamallakin kafar, Alhaji Ibrahim Makama ya fitar.
- 2023: Daga Karshe Dai Tawagar Su Dogara Sun Mara Wa Atiku Baya
- Alfanun Noman Gyada Wajen Habaka Tattalin Arzikin KasaÂ
Shawai, dai ya kasance na tsawon shekara uku da rabi a matsayin kakakin kamfanin raba wutar lantarki na Kano (KEDCO), yanzu haka kuma zai kama aiki a matsayin sabon manajan gudanarwa gidan talabijin din daga ranar 1 ga watan Janairun 2023.
A sabon aikin nasa, ana tsammanin Shawai zai jagoranci gudanar da harkokin kamfanin na yau da kullum, kuma zai jagoranci sauran daraktocin kamfanin wajen gudanar da ayyukan gidan talabijin din.
Sannan, zai kasance mai fitar da tsare-tsaren da za su tabbatar da bin ka’idoji da dokokin hukumar gudanar na kamfanin.
Kamfanin, Tambarin Hausa TV ‘Amon Gaskiya’ na daya daga cikin gidajen talabijin da suka samu tagomashi a duniya masu yada shirye-shiryen su da harshen Hausa.
Shawai, dan jarida ne haifaffen Jihar Kano, ya yi aiki a kafafe da dama na ciki da wajen kasar nan a bangaren yada labarai kuma yana da gogewa sosai a bangaren aikin na jarida.