Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta tabbatar da faduwar wani tankin ruwa a kan mutane biyu har suka rasa rayukansu a yankin Ladi Lak, Bariga a Jihar Legas.
Ibrahim Farinloye, Kodinetan shiyyar Kudu-maso-Yamma na NEMA, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) faruwar lamarin a ranar Lahadi.
- Korafin Dogara Kan Yunkurin Kasheshi: Muna Kan Bincike Ne Har Yanzu, Amma Mun Kama Mutum Biyu – Kwamishinan ‘Yansanda
- Fim Sana’a Ce Mai Alfarma Da Albarka – Ibrahim Gungu
Farinloye, ya ce tankin ya fado ne daga wani bene mai hawa biyu har ya fado a kan wasu maza su biyu, babba da yaro, yayin da wasu manya uku suka samu raunuka.
Ya ce shugabannin al’umma na yankin Bariga ne suka kai wadanda suka jikkata asibiti kafin isowar jami’an agajin gaggawa.
Ya ce lamarin ya faru ne a titin Adeleye, Ladi Lak, Bariga, wani yanki na Legas.