Wata tawagar yawon shakatawa ta Sinawa 20, wadanda suka bi jirgin saman kasar Habasha, ta isa filin jirgin saman kasa da kasa na Kilimanjaro dake Tanzaniya, kuma tawagar ta zama ta masu yawon shakatawa ta farko da ta ziyarci Tanzaniya, tun bayan da kasar Sin ta yi gwajin farfado da harkokin yawon shakatawa a ketare.
Damasi Mfugale, babban daraktan hukumar yawon shakatawa ta kasar Tanzaniya, ya yiwa tawagar matukar maraba da isar kasar. Ya ce, Tanzaniya kasa ce mai ni’ima, kuma mai arzikin albarkatun namun daji, da tsire-tsire da al’adun gargajiya. Ya ce zuwan tawagar yawon shakatawa ta kasar Sin, wani muhimmin ci gaba ne a fannin kara karfafa dangantakar al’adu, da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Kaza lika a cewar jami’in, sana’ar yawon shakatawa na daya daga cikin ginshikan tattalin arzikin Tanzaniya. Kuma a cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta kasance muhimmiyar kasa dake samar da dimbin masu yawon bude ido ga sana’ar yawon shakatawa ta Tanzaniya. (Safiyah Ma)