Ministocin harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai zasu tattauna batun kara lafta wa Rasha takunkuman karayar tattalin arziki, tare da karin tallafin makamai ga kasar Ukraine a taronsu na yau Litinin, a cewar majiyoyin diflomasiyya.
Tun da farko rahotanni sun ce Tarayyar Turai na shirin kara kakaba wa Rasha jerin takunkumai na bakwai da suka hada da haramcin sayen zinare daga Rasha a karshen wannan watan.
- An Dakatar Da Sarkin Da Ya Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A Zamfara
- Sabon Gwamnan Osun: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ademola Adeleke
Sai dai majiyoyin sun ce babu wani hukunci da za a yanke a Litinin, sai a mako mai zuwa.
Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turan za su tattauna batun bai wa Ukraine damar takarar neman shiga kungiyar, gabanin taron kungiyar na ranakun 23-24 ga wannan wata.
Ana ci gaba da tafka yaki tsakanin Rasha da Ukraine, wanda dubban mutane suka mutu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp