A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin duniya na kin mafarkin murdiya. Tarihi ya nuna mana cewa, tabbatar da adalci ya kasance alkiblar al’ummar dan Adam ta dindindin. Ko da yake a wani lokaci mugunta ta samu damar mai da hannun agogo baya, amma a karshe abubuwa za su koma daidai.
Sama da shekaru 80 da suka gabata, lokacin da motocin yaki na Jamus suka murkushe kauyuka a kasashen gabashin Turai, kuma jiragen saman yaki na Japan suka jefa bama-bamai a kasar Sin da mai da biranenta zuwa kufai: da alama kasashen sun kasance masu karfi da ba za su taba shan kaye ba. Amma a karkashin turjiyar mutane masu adalci na duniya, ‘yan mulkin zalunci ba za su iya magance faduwar totuwa da fuskantar hukunci a karshe ba. Mugunta ba za ta iya lashe adalci ba, wannan yana cikin ka’idojin tarihi.
- Ana Zargin Jami’in Sibil Difens Da Harbe Abokin Aikinsa A Abuja
- Neman Gurbi: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Afirka Ta Kudu A Bloemfontein
Sai dai har yanzu, bil’adama suna ci gaba da fuskantar ayyukan dake neman mai da hannun agogo baya: tunanin mulkin danniya, da ra’ayi na daukar matakin kashin kai, da na kariyar ciniki, suna yaduwa a duniya. Wasu kasashe sun kaddamar da yakin cinikayya da na haraji, wadanda suka yi matukar illata tattalin arzikin duniya da kuma karya dokokin cinikayya na kasa da kasa. Amma masu kare adalci suna nan a ko da yaushe, wadanda ke kokarin mayar da duniya kan turba mai dacewa, kuma kasar Sin na daya daga cikinsu.
A gun taron kolin BRICS da aka gudanar jiya ta yanar gizo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda uku a cikin jawabinsa: Wato tsayawa kan manufar cudanyar sassa daban-daban, da kiyaye daidaito da adalci a duniya; da tabbatar da bude kofa da cin moriya tare, don kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa; da kuma tabbatar da hadin kai a kokarin samun ci gaba na bai daya. Wadannan shawarwari, sun kunshi kalmomi na nuna sassaucin ra’ayi, amma ma’anarsu na cike da adalci. Suna wakiltar martanin kasar Sin game da yunkurin mayar da hannun agogo baya da ake fuskanta a halin yanzu a fagen kasa da kasa, wadanda ke nuna yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da adalci, da neman hadin kai, da sa kaimi ga tabbatar da moriyar juna a duk fadin duniya. Wannan tsari na adalci shi ne ainihin dalilin da ya sa kasar Sin samun cikakken goyon baya daga mafi yawan kasashen duniya.
Tabbas, ya kamata a kiyaye adalci ta hanyar aikace-aikace maimakon magana. Mu dauki yakin haraji da Amurka ta kaddamar kan Afirka a misali: Bayan da Amurka ta sauya manufarta ta ciniki da kasashen Afirka, da sanya musu harajin fito mai yawa da ya kai kaso 15 zuwa kaso 30 cikin 100, nan da nan kasar Sin ta fara taimakawa kasashen Afirka, inda ta sanar da cewa, za ta yafe dukkan harajin da ake karba kan kayayyakin da kasashe 53 dake nahiyar Afirka, wadanda suka kulla hulda da ita, suka fitar zuwa cikin gidanta. Wannan matakin ya aike da wani sako mai kyau ga Afirka, wato kasar Sin na son raba damar samun ci gaba tare da kasashen Afirka, da hadin kai da su don tinkarar hadurra. Lamarin da ya samu yabo daga masana tattalin arziki na kasashen Afirka.
Kana wasu alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashe mafi karancin ci gaba a nahiyar Afirka, wadanda Sin ta riga ta yafe musu dukkan haraji, ta kai dalar Amurka biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara. Ta hanyar karfafa hadin gwiwar cinikayya da abokan hulda kamar Sin, da inganta cinikayya a cikin nahiya, ana sa ran ganin Afirka za ta samu nasarar rage tasirin manufar harajin Amurka.
A halin yanzu, kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin da kasashen Afirka, suna kokarin daukaka ra’ayin cudanyar sassa daban daban, da na bude kofa, da yin hadin gwiwa tare da tabbatar da moriyar juna, da hadin kai da juna, a karkashin laimar tsare-tsaren hadin gwiwa irin na BRICS, kuma suna tafiya zuwa gaba kan wata turba mai adalci. Tabbas babu wani karfi da zai iya hana su cimma buri da samun nasara. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp