A shekarar 1934 kwamitin gwamnatin Arewacin Nijeriya ya ba da shawara ga kwamitin zartarwa cewa a kirkiro wurin bude ido da shakatawa da wucin gadi a masarautar Bauchi. Alhaji Muhammadu Ngeleruma, shi ne Ministan aikin gona da albarkatun kasa karkashin tsohuwar gwamnatin Arewa ya ji dadin wata tafiyar da ya yi zuwa filin shakatawa da bude ido na kasar Sudan lokacin da ya je aiki a Afirka ta gabas.
Lokacin da ya dawo sai ya ba da shawarar a bude irin shi a Nijeriya.
A shekarar 1956 gwamnatin Jihar Arewa ta amince da shirin da aka yin a samar da wurin da za a kafa wurin shakatawa da bude idanu. Sai aka amincewa da sunan Yankari a matsayin wurin da yafi dacewa a Kudu a wancan lokacin ana kiran wurin Lardin Bauchi inda akwai manyan namun daji da yawa wadanda wurin suke zama za kuma a kare su. A shekarar 1957 ne aka ware wurin inda aka sa ma shi suna a karkashin hukumar kulawa da gandun daji ta Bauchi.
- An Gano Ciwon Ciki Da Ke Turnuke Sojojin Isra’ila A Gaza
- Kungiya Ta Yi Kira Da A Gaggauta Bincike Kan Harin Soji A Kauyen Tudun Biri
An bude Yankari a karo na farko ga mutane a matsayin wurin shakatawa na Firimiya ranar 1 ga Disamba 1962. Tun wancan lokacin ne gwamnatin Arewacin gabashin da jihar Bauchi tare suka fara kulawa da wurin.
Wurin shakatawa ko bude ido naYankari wani babban wurin yawo bude ido ne ko shakatawa da ya taba kasancewa a karkashi gwamnatin tarayya a kudu maso tsakiyar Jihar Bauchi a sashen Arewa maso gabas na Nijeriya.
Wuri ne mai tsawon murabba’in kilomita 2,244 km2 (866 sk mi),bugu da kari wurine na abubuwa masu burgewa da ban sha’awa.Yana a cikn yanayin da zai burge da kayata mutane saboda kasancewar inda yake yammacin Afirka inda yake da dabbobi wadanda wurin ka same su.Wurin shakatawa ko bude ido na Yankari an kirkiro shi ne a shekarar 1956 tun kafin a samu mulkin kai, amma daga baya an mai da shi babban wurin shakatawa na kasa a shekarar 1991.Wurin shakatawa ne wanda ya yi suna wajen baki da su zo yawan bude ido a Nijeriya, ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa harkar shakatawa da abubuwa masu daukar hankali da aka same su a wurin.
Wurin shakatawa na Yankari kauyuka sun zagaye shi da suke da manoma da makiyaya, sai dai kuma ba wani abin da ya nuna dan Adam ya taba zama a wurin fiye da shekaru dari da suka wuce. Sai dai kuma akwai alamun da suke nuna mutane sun taba zama a wurin da suka hada da,tsofaffin karafa da wani wurin da ake samar da wuta ta yin aiki, duk da yake a karshen shekarar 1990 akwai irin abubuwan fiye da hamsin a Delimiri da Ampara.