ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Gusau Da Sarakunanta (2)

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
Gusau

Gusau ita da wasu wuraren da suke makwabtaka da ita an mika su ga Mallam Sambo Dan Ashafa sun kasance ne a cikin birnin na masarautar.A Gusau bayan ta kasance karkashin Mallam Sambo da hedikwatarta take a Gusau tana da wasu garuruwa da suke har ila yau karkashin Wonaka, Mada, Yandoto, Samri, Magami, Marabu, Mareri, Mutumji, Kwaren Ganuwa, Wanke da wasu kauyukan da suke zagaye da Gusau, kamar sauran sassan na daular Usumaniyya.

Ta hanyar lamarin tafiyar da mulki bayan da akwai wadanda suke taimakawa ita Gusau din wajen tafiyar mulki, har ila yau sai unguwanni biyar, bayan da aka kasa shi garin Gusau din zuwa unguwanni ko shiyya kamar yadda sunayen su suke  haka,Shiyyar Magaji, Uban Dawaki, Galadima, Mayana da kuma Sarkin Fada. Sune suke wata kafa da take sada al’umma tsakaninsu da Dagatai ko masu unguwanni,da kuma Sarkin katsinan Gusau (Emir Of Gusau).Su ne suka kasance kunnuwa da kuma idanun Sarki.Gusau kamar sauran sassan da suke karkashi daular Usumaniyya suna aikawa da kason fadar Sarkin musulmi na irin kudaden da ta samu.

  • Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
  • Har Yanzu Tukunyar Rikicin Masarautar Kano Na Tafarfasa

Bayyanar mulkin mallaka na Turawa ya kawo nau’oin cigaba na garin Gusau da kungiyoyin da suke cikin birnin. Abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da aka sa ma kwalta, hanyar jirgin kasa, manyan kantuna, da wasu harkoki, manyan kamfanoni duk an kawo ma shi birnin da haka ne kuma Gusau ta kara samun bunkasa ta cigaban zamani.

ADVERTISEMENT

Sai dai duk da haka wasu tsare- tsaren mulkin mallaka da aka kawo sune suka sauya salo na mulkin.Idan ba haka b agarin na Gusau bai kai a rika  ba shi girma da daukaka ba, amma sai ga shi cikin kankanen lokaci lamurra sai suka canza.Lokacin mulkn mallaka na turawa ne aka fa amsar harajin dabbobi a shekarar 1907 da ake kira da suna  (Jangali).

Zamanin mulkin mallakar ne sana’ar noma ta kasance babbar abar da take bunkasa tattalin arziki na garin Gusau,abin kuma sai ya kara bunkasa garin ya kasance na manoma.Sana’ar noma ta zama ba tad ana biyu idan ana maganar tattalin arziki ne wadda ake yi da Damina wajen noma kayan amfanin gona a ci da kuma sayarwa

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)

Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai

 

Jerin Sunayen Sarakunan Gusau

Malam Sambo Dan Ashafa 1806- 1827

Wadannan Sarakunan shida na daga cikin zuri’ar Sambo Dan Ashafa kamar haka:

Malam Abdulkadir 1827-1867

Malam Muhmmadu Modibbo 1867-1876

Malam Muhammad Tuburi 1876-1887

Malam Muhammadu Gide 1887-1900

Malam Muhammadu Murtala 1900-1916

Malam Muhammadu Dangida1916-1917

Sai dai kuma daga shekarar 1917 zuwa 1984 ba a bayyana sunayen Sarakunan da ba.

Alhaji Muhammadu Kabir Danbaba Sarkin Katsinan Gusau 1984- 2015

Alhaji Ibrahim Bello 2015 zuwa yanzu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)
Masarautu

Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)

January 12, 2025
Alh. Hassan Baita Ubawaru (Ma'ajin Hausawan Turai)
Masarautu

Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai

July 31, 2024
Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa
Labarai

Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa

July 22, 2024
Next Post
Ku Daina Alaƙanta Ni Da Ƴan Bindigar Zamfara – Matawalle Ya Gargadi Yan Adawa

Ku Daina Alaƙanta Ni Da Ƴan Bindigar Zamfara - Matawalle Ya Gargadi Yan Adawa

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

November 14, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

November 14, 2025

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

November 14, 2025
Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

November 14, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

November 14, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.