A lokacin da Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Makau ya fita ya zuwa Sallar Idi. Su Wadancan masu bore sun rufe kofar Gari suka hana shi komawa cikinta.
A dalilin haka Sarki Muhammadu Makau sai bai wani ja da su ba, domin a tunaninsa jama’arsa ne kuma bai da bukatar yakar kasarsa, amma sai ya juya akalar dokinsa ya nausa cikin kasashen Nufawa da sauran kabilu don bude wata daula daban.
- An Bude Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Sin Karo Na 4
- Kwastam Reshen Tashar Jiragen Ruwan Apapa Ta Tara Naira Biliyan 489 Cikin Wata Uku
Kafin ya bar kasar Zazzau ya yi dakata a bayan gari inda ya tattara jama’arsa.
Wancan wuri a yau shi ake kira da suna Dakace (Dakacen Sarki).Ya cimma nasarar yin hakan wajen kafa wuri (wuraren da a yau suka zama masarautu biyu wadanda ake kiransu da sunayen kannensa a halin yanzu wato Sule-ja (Sulaimanu- sza) da Abu-ja (Abubakar- sza).
Wancan wurin ne a yau ya zama zuciyar kasar baki daya.Tarihi ya nuna cewar daga baya ya yi yunkurin fadada sabuwar daularsa ta wajen yakar ko kwatar wasu bangarori na kasar Zazzau duk da a lokacin tsufa ya kama shi sai ya umurci danuwasa Sulaimanu Ja da ya koma ya rike sabuwar daularsa gudun kar ta kubuce masu baki daya; inda ya sa shi a matsayin wakilinsa.
Bayan rasuwar Sarki Muhammadu Makau sai Malam Sulaimanu ya zama sabon sarki.
Wannan wuri daga baya an raba shi biyu inda su wadancan kanne na Sarkin Zazzau Muhammadu Makau suka mai da su wuraren masarautunsu kuma aka sanya wa wuraren sunayensu.
Dalilin raba wa ‘yan-uwasa wannan wuri zai ta’allaka a kan samar da zaman lafiya a zuriyarsu kuma su shugabanci wadannan sabbin dauloli don kauda tunaninsu ga komawa cikin birnin Zazzau.
Wannan ba karamin tunani ne ba, ga shugabanni adalai masanan ya kamata da hangen nesa.
Daga wa]annan wurare basu sake tunanin kafa wata daula ko fadada kasa ba.Sai dai tarihin baya na shi Sarki Muhammadu inda ya yi yunkurin kwato wasu yankuna da ke karkashin kasar Zazzau ya zuwa sabuwar masarautarsa kuma wannan yunkuri ya cimma ajalinsa.
Shehu ]an Fodio ya yi fama da jama’arsa ko ince mabiyansa a }arken jihadinsa.Domin sun juya al’amarin ya zuwa neman mulki ba wai kokarin da’awa da jaddada addinin Allah; da daukaka addinin Allah ba.
Almajiran Shehu sun mai da hankali wajen neman mulkan jama’a ko ta halin ya ya.
Manufar Shehu shi ne na kauce wa shirka da kadaita Allah (S.W.A) abin bauta shi kadai kuma su maida duk al’amurransu ga Allah shi kadai.
Amma‘yan shirkokin da ba a rasa su ba tun daga mabiyansa har ya zuwa ga sauran jama’a. Allah (subhanahu wata’ala) ya sa ya cimma nasara ta dagewa a kan akidarsa ba tare da jin tsoro ko shakkun wani abin da zai same shi ba.
Duk wadancan nasarori sun samu ne ta wajen dagewar da Shehu tare da kaninsa Abdullahi da kuma dansa Muhammad Bello, su ka yi bisa yardar Allah.
Mahara daga cikin daliban Shehu Mujaddadi,wadanda son mulki ta yaudara, sun tafi ya zuwa kasashen Borno da Yobe da Taraba da kuma Bauchi, inda suka tarad da Malam Rabeh Fadel Allah ya yi nisa da shigowa wajan jihadinsa.Wannan za a iya gani tun daga cikin kasar Nijer har ya zuwa kasashen da na yi bayani a baya.
Kamar yadda tarihi ya nuna mana cewar kafin karshen jihadin da gudana a zamanin Shehu Usmanu, dalibansa sun yi yunkurin kai jihadinsa kasashen gabashin kasashen Arewa wanda bai samu dama ba don tuni addini Musulunci ya yi karfi sai dai fadan siyasa kawai.
A littafi mai sun “ Language Disappearance, case study of Biu Emirate” na Bukar Usman ya yi kokarin bayanin yadda ta kwashe tsakanin Mujaddadi Rabeh Fadel Allah tare da dansa Fadarallah da masarautun wadannan kasashe a tsakanin shekara ta 1755zuwa 1809.
Rabe ya nausa kasar Borno dansa kuma ya nausa }asar Biu har ya zuwa Wuyo wanda ake kira da suna Bayo a halin yanzu cikin kasar Borno.
Wannan ya faru ne a tsakanin shekarar 1893 zuwa 1901. A dalilin wannan tashin-tashina na jahadin wanda wadancan Shehunnai biyu suka yi, ya kawo kai-komon jama’a daga wannan waje zuwa wancan waje,musamman ga jama’ar Biu a wancan karni.
Hujjojin wannan bayani an samo su ne ta wajan zantawa da jama’a daban daban, wanda ya nuna cewar jama’a sun taru daga Arewacin masanin ba a gabashin Nijer da Borno zuwa kudancin wannan kasa. Misali jama’ar Biu sun nuna cewar akwai wurare biyu wanda yake duk asalin wurin mazaunansu ne (wurin zamansu),kamar Yemen da Chadi.
Majiya:- Hausa Wikepedia