A yau daya daga cikin wadancan wurare mai suna Abuja ta zama abin alfari ga kasar Nijeriya baki daya, inda ta zama abin tunkahon jama’ar Nijeriya a matsayin Gundumar mulkin kasa baki daya.
An amshi wannan wuri (Abuja) a hannun Sarki Sulaimanu Barau a matsayin gundumar mulkin kasa a shekara ta 1976.
- Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?
- Nijeriya Na Kara Kaimin Bunkasa Sufurin Jiragen Sama Ta Hanyar Fasahar Tauraron Dan’adam – Keyamo
A nan zamu iya ganin yadda aikin Sarki mai adalci Muhammadu Makau dan Sarki Isyaku Jatau ya kai. Wannan ba karamin abin alfahari ne ba.
Zazzagawan dauri wato na da can sun ci gaba da huddarsu da Fulani da ke makwabtaka da su,masu zama a Bida. Amma jama’ar da ke kasar Zariya sun komo da hujja da sabuwar kasar Muhammadu Makau dole a zamanin Sarki Abubakar Kwakwa, daga shekara ta 1851 zuwa 1877.
Fadar sarki
Wannan ya faru a dalilin tsaida duk wani nau’in kasuwanci tsakanin kasar da kudancin Nijeriya.
Bayanan abubuwan da suka wakana a tsakanin ma su da’awar karbar tuta daga hannun Shehu Usmanu na tattare a gun wadanda abin ya shafa,inda za ka iya samun gaskiyar abin da ya gudana a tsakaninsu. Amma ga al’amarin Hausa-Fulani ba za su tsaya su tsage gaskiya don kowa ya ganta ba, illa su bayyana cewar sun kori kafurai ko su yi amfani da kalmar maguzanci.Allah mai girma, in muka ce za mu yi maganar irin nau’in mulkin da suka yi wa jama’a tabbas mutunci da kimatsu za su zuba a idon jama’a musamman ‘yan bana-bakwai. Domin in aka fassara kalmar Maguzanci kuma aka duba ta daya bayan daya zamu ga irin mummunar zaman da aka yi ko ince a ke yi da su, in da hatta su kansu ba su bar junan su ba. Bari mu ga wani abu daga cikin al’amurran da suka faru a yake-yaken jihadi ko son mulki sun ci gaba da gudana kuma jama’a sun ci gaba da hijira daga wannan wuri zuwa wancan wuri har ya zuwa shekara ta 1808 inda Fulani suka kama yammacin Ngazargamu wanda yake shi ne birnin daular Borno. Amma daga karshe a cikin shekara ta 1809 Sheikh Lamido ya kori Hausa-Fulani daga daular Borno.
Masarautar Zazzau
Babbar kofar shiga masarautar Zazzau da ke Zariya
Zazzau ko Zariya Masarauta ce t mai dadadden Tarihi ta Hausawa wadda ta ke da gidan sarautar ta a birnin Zariya a jihar Kaduna a Arewacin Najeriya . Alhaji Shehu Idris Shine Sarkin Zazzau a wancan lokacin.
Maguzanci
Abu mafi mahimman ci da zamu fara dubawa wajen gane tarihin masarautar Zazzau shine labarun da suka shahara a karni na ashirin. Wanda yake nuna cewa asalin kafuwar masarautun Hausa abin ya fara ne daga kanen Bayajidda,Wato wani Jarumi da ake fada a tarihin Hausawa wanda shine asalin kafuwar masarautun Hausa da muke da su a wannan zamanin.Kamar yadda masana Tarihi suke fada cewa a karni na goma sha daya ne aka kafa masarautar zazzau bisa jogorancin Sarkin Zazzau Gunguma.Daga nanne kuma aka kafa masarautar Zazzau ta zama daya daga cikin masarautun Hausawa ko Habe na Hausa Bakwai.Fitacciyar wadda tayi iko a masarautar Zazzau it ace Sarauniyar Zazzau Amina.
Wacce tayi iko ko dai tsakiyar karni na sha biyar ko kuma tsakiyar karni na sha shida. Birnin Zazzau ya zama cibiyar harhada bayi inda ake cinikin su zuwa Arewacin Najeriya kamar birnin Kano da birnin Katsina inda ake kasuwancin Bayi ta hanyar kasuwancin ban gishiri na baka Manda daga nan kuma sai a wuce da Bayin zuwa Sahara.A yadda tarihi yazo Musulunci ya shiga Masarautar Zazzau ne a wajen shekara ta 1456 amma kadan daga cikin wasu mutanen na ci gaba da tsafi yayin da wadansu kuma ke Maguzanci Har zuwa lokacin da jihadin Shehu Usman Dan fodiyo ya zo a shekarar 1808. Ayanzu dai Masarautar Zazzau Masarauta ce da ta yi kaurin suna wajen tafiyar da Addinin Musulunci.Akwai manya manyan malamai na Musulunci a Masarautar.
Sarautar Fulani a Masarautar Zazzau
A watan Disamba na 1808 Mujahidai karkashin Jahorancin Mujadda Shehu Usman Danfodiyo suka samu nasarar korar Masu rike da sarautar lokacin wadanda Habe ne ko Hausawa.Hakanne yasa su Hausawan suka gudu zuwa yankin Abuja Suka tare a wajen da ake kira Suleja a yanzu.Shi yasa har yanzu ake kiran sarautar ko kuma sarkin Suleja da Sarkin Zazzau. Tarihin Bayajidda wanda a yau masana na kallonsa a kagaggen labari domin tambayoyin da ke kansa sun kasa amsuwa. Amma in muka kalli manufa ta wannan labari zamu ga cewar an samar da shi ne don samar da zaman lafiya tsakanin kasashen Hausa.In muka kalla ta bangaren nazartar harshe zamu ga wannan tarihi bai da hurumin ko kusa musamman in muka kalli kalmomi da ke rataye da kasar Zazzau.
An samo wannan Tarihin ne daga encyclopedia ta Hausa