Shi dai Muammar Gaddafi, shi ne tsohon shugaban kasar Libya, ya rayu daga shekara ta 1942 zuwa 20 ga watan Oktoba shekara ta 2011), Muammar al-Gaddafi da larabci:
Am fi saninsa da Kanal Gaddafi ko Gaddafi, ya kasance dan gwagwarmayar kasar Libya ne, Dan siyasa, kuma mai taimakon mutanensa.
Ya mulki kasar Libiya matsayinsa na jagoran juyin mulkin da ta samar da Jamhuriyyar Larabawa ta Libya wato Libyan Arab Republic da turanci, tun daga shekara ta 1969 har zuwa 1977, sannan aka canja sunan jagorancinsa zuwa Shugaba Dan’uwa wato “Brotherly Leader” na babbar jam’iyar talakawa, da akafi sani da Great Socialist People’s Libyan Arab Jamahiriya tun daga shekara ta 1977 har zuwa shekaran 2011.
Gaddafi ya kasance dan rajin ci gaban Larabawa ne amma daga baya ana ganin ya watsar da hakan ya fara bin ra’ayin kansa.
Gaddafi ya rike mukamai da dama a ciki da wajen kasarsa, daga ciki ya rike shugaban kungiyar kasashen Afirika wato African Union (AU) daga 2 ga Fabrairun shekarar 2009 har zuwa 31 ga watan Janairu. Gaddafi ya yi karatunsa a Jami’ar Kasar Libya da kuma Jami’ar Soji ta Benghazi, Gaddafi Musulmi ne, mai bin ahlus-Sunnah, wato sunni Islam.
Tarihinsa.
An haifI Gaddafi a kusa da garin Sirte daga gidan talakawa makiyayan Larabawa, Gaddafi mai matukar kishin Larabawa ne tun yana makaranta a Sabha, daga nan ya shiga Royal Military Academy, Benghazi.
Yana cikin soja ne ya hada kungiyar da ta kifar da mulkin Turawan Yamma a kasar wanda suke amfani da sarkin kasar na wancan lokacin wato Senussi Mulkin Idris a shekarar 1969.
Daga amsar mulki, Gaddafi ya sauya Libiya daga mulkin sarauta zuwa jamhuriyya inda ‘yan gwagwarmayarsa ke mulki da umurninsa.
Daga nan ne ya kora dukkani Italiyawa da Turawan dake da sansani a kasar zuwa kasashensu, kuma ya karfafa dangantakarsa da sauran kasashen Larabawa, musamman da Shugaba Gamal Abdel Nasser’s na kasar Misra (Egypt) tare da neman hadin kan kasashen Afirika.
Gaddafi ya kafa Shari’a a matsayin abin gudanar da dokokin kasar, tare da daukar tsarin jagoranci Musulunci.
Ya mayar da arzikin man fetur din kasar mallakar gwamnati kuma ya rika amfani da kudaden domin karfafa sojojin kasar, da taimaka wa kasashen waje, da taimaka wa mutane wurin ginin gidaje, kiwon lafiya, ilimi da sauransu.
Gaddafi ya sauya fasalin Kasar Libya zuwa mulkin da ya kira “Jamahuriyya” wato kasar al’ummah da Turanci (“state of the masses”) a shekarar 1977.
A shekara ta 1970s zuwa 1980s, yakin iyaka tsakanin Libya da kasashen Misra da Cadi da taimakon ‘yan tawayen kasashen waje, da zargin da ake masa na daukar nauyin Lockerbie bombing a kasar Scotland ya sa kasar ta zama saniyar ware a duniya.