Hukumar kulawa da al’amarin kudi ta Afirka ta yamma ita ce ke da alhakin ba da takardun kudi a Nijeriya daga shekarar 1912 zuwa 1959, kafin dai wannan lokacin Nijeriya ta yi amfani da kudade daban- daban da suka hada da “Wuri da Manilas.
Ranar 1 ga watan Yuli 1959 ne Babban Bankin Nijeriya ya fitar da tsaba da takardun kudi na Nijeriya daganan sai aka janye na Afirka ta yamma.Amma 1 ga Yuli 1962 lokacin da Nijeriya ta zama jamhuriya,an sake sauyawa domin la’akari da aka yi da hakan. An sake canza kudin a shekrar 1968 a matsayin wani mataki saboda yadda ake amfani da takardar kudin ta hanyar da bata dace ba.
- Amaechi Ga ‘Yan Nijeriya: Akwai Dan Siyasar Da Ya Taba Ce Muku Shi Ba Barawo Ba Ne?
- Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wang Yi
31 ga Maris 1971 Shugaban kasa na mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya bada sanarwar Nijeriya za ta canza kudinta daga ranar 1 ga Janairu 1973 inda za a rika kiran takardar kudin da suna Naira zaba kuma za a kira shi da suna Kobo inda shi Kobo 100 yana dai dai da Naira daya. Matakin canza kudin an dauke shi ne bayan shawarwarin da kwamitin da aka kafa a shekarar 1962 ya gabatar da rahotonsa a shekarar 1964.
Canjin da aka yi a Janairu 1973 babba ne domin kuwa ya shafi dukkan takardar kudin da tsabar wadanda tun farko ana amfani ne da da fam daya na Ingila aka bar amfani da shi. Ya yin da Naira daya tana daidai da sulai goma.
Ranar 11ga Fabrairu 1977 aka yi sabuwar takardar kudi ta Naira 20 aka fitar da ita ta musamman ce domin tana da muhimmanci ta fuskoki biyu.
Naira ashirin 20 ita ce babbar takardar kudi da aka fitar 1977 dalilin samar da ita shi ne abin ya zama dole ne idan aka yi la’akari da ana samu karuwar kudaden shiga a Nijeriya, domin a samu saukin wajen harkokin da suka shafi kasuwanci.
Naira ashirin it ace takardar kudi ta farko da take dauke da hoton mutum dan asalin Nijeriya, shi tsohon Shugaban kasa na mulkin soja Janar Murtala Ramat Muhammed d a aka haifa 1938 ya rasu a shekarar1976 mutum ne da ake yi ma Kallon ya kawo sauyin tafiyar da al’amuran gwamnati a watan Yuli 1975.
Ranar 2 ga Yuli na shekarar 1979 an kara yin wasu sabbin takardun kudi na Naira1, Naira 5, da Naira 10, a shekarar In 1992 kobo 50 da Naira 1 an mai da su tsaba.Bugu da kari saboda yadda tattalin arziki yake bunkasa da al’amarin saye da sayarwa an yi sababbin takardun kudi na Naira 100, Naira 200, Naira 500 da Naira1,000 a watannin Disamba 1999,Nuwamba 2000, Afrilu 2001 da Oktoba October, 2005.