Gwagwarmayar zanga-zanga a Nijeriya, ta samo asali ce tun lo-kacin mulkin mallaka; inda dandazon mutane suka yi dafifi kan manyan hanyoyi, don nuna rashin amincewarsu da wasu kudire-kudire da kuma salon mulkin Turawan Mulkin Mallaka.
Gwamnatin Turawan Mulkin Mallaka, ta yi matukar mamaki da ganin yadda mata daga gundumar Bendel; wato Abiya kenan suka fito a shekarar 1929, wanda daga bisani aka kira ta da zanga-zangar mata ta Aba, don nuna rashin amincewa da rash-in sanya mata cikin harkokin gudanar da gwamnati; ta hanyar sammacin shugabanni.
- Shugaban Timor-Leste Ya Yaba Kayayyaki Kirar Kasar Sin
- Nijeriya Na Kashe Dala Miliyan 600 Wajen Shigo Da Mai Duk Wata – Minista
Kazalika, akwai kuma zanga-zangar matan Abekuta, wanda kungiyar matan Abekuta ta shirya a shekarar 1940; don nuna rashin amincewa da harajin da Turawan Mulkin Mallakan suka kakaba na rashin adalci.
Haka nan, sai da wannan zanga-zanga ta zama ruwan dare a Nijeriya; har zuwa lokacin samun ‘yancin kai, inda kungiyoyi da dama suka rika yin kiraye-kiraye da babbar murya, don cimma biyan bukatunsu.
A shekarar 1964, an samu mummunar hatsaniya a yankunan Tibi, sakamakon kakaba musu biyan haraji da aka yi na babu gaira babu dalili; wanda zanga-zangar ta yi sanadiyyar rasa dimbin rayuka da dukiyoyi.
Har ila yau, a lokacin mulkin sojoji; kungiyoyin kwadago da na dalibai da sauran kungiyoyin al’umma, su ne kan gaba wajen jagorantar kowace irin zanga-zanga.
A tarihin zanga-zangar, akwai lokacin da daliban makaranta su-ka jingine karatunsu tare da shiga zanga-zanga; daidai lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo; sakamakon cire tallafin karatunsu.
Kazalika, akwai lokacin da daliban suka sake jagorantar wata babbar zanga-zanga a 1989, lokacin da Janar Ibrahim Ba-bangida ya bullo da shirin nan na SAP (Structural Adjustment Programme).
Bugu da kari, masu rajin kare hakkin al’umma da masu son tabbatar da mulkin dimokradiyya, sun tara mutane da dama; don neman ‘yancinsu na dawo da mulkin farar hula, yayin da gwamnatin mulkin soja ta Babangida; ta yi kamar ta yi watsi da alkawarin da ta yi na mika wa gwamnatin dimokradiyya.
Haka wannan zanga-zanga ta yi ta faman afkuwa a lokuta daban-daban na shugabannin Nijeriya, tun daga lokacin mulkin mallaka, sojoji har kawo yanzu da muka samu kanmu a mulkin dimokradiyya ko na farar hula.