Jiya, manyan kusoshin kasar Sin sun kira wani taro don tattauna batun raya tattalin arziki, inda suka sa ran cika burikan da aka tsara, ta fuskar raya tattalin arziki da zaman al’umma a shekarar 2024. Kana sun gabatar da shirin raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2025, mai kunshe da matakan harkar kudi masu yakini, da na raya kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da masana’antu, da sa kaimi ga aikin sayayya, da dai makamantansu.
Wadannan matakai masu yakini sun sa mutane masu sayen hannayen jari na kasashe daban daban, yin imani da yanayin tattalin arzikin Sin. A jiya, ma’aunin darajar hannayen jarin kamfanonin kasar Sin a kasar Amurka da aka san shi da NASDAQ Golden Dragon China, da kuma ma’aunin Hang Seng na yankin Hong Kong na kasar Sin sun karu sosai. Kana a yau, darajar hannayen jarin kamfanoni fiye da 5200 dake kasuwar babban yankin kasar Sin su ma sun yi ta karuwa.
- Jami’ar Kwara Ta Rage Wa Masu Bukata Ta Musamman Kudin Karatu
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
Yadda manufofin kasar Sin a fannin tattalin arziki suka haifar da tasiri mai yakini a kasuwannin duniya bai ba mutane mamaki ba, saboda tun kafin kaddamar da sabbin matakan bunkasa tattalin arziki a kasar Sin, kwararru masu nazarin tattalin arzikin Sin sun dade suna nuna wa kasar Sin cikakken imani kan makomar tattalin arzikinta. A ganinsu, kasar Sin ta iya daidaita manyan tsare-tsaren tattalin arziki yadda take bukata, abin da ya sa ta kasancewa cikin yanayi mai karko duk lokacin da aka samu tangal-tangal na yanayin tattalin arzikin duniya. Wannan ra’ayi ya zama daya da abun da wani sharhin da aka wallafa a jaridar “The Guardians” ta kasar Najeriya a kwanakin baya ya kunsa, inda aka ce, yadda gwamnatin kasar Sin ke tinkarar kalubaloli cikin yakini, ya sa ta samun cikakkiyar jajircewa a fannin raya tattalin arziki, da samar da gudunmowa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
Hakika, kafin a yi imani da wani mutum ko wata kasa, dole ne ya/ta zama mai cike da imani da kai. A wajen wani taron neman tattara shawarwari daga manyan jami’an jam’iyyu daban daban na kasar Sin, da ya gudana a kasar a kwanan nan, shugaba Xi Jinping na Sin ya jaddada muhimmancin nuna imani kan samun ci gaban tattalin arziki. To sai dai kuma ko ta yaya za a iya samun imanin? Shugaba Xi ya ambaci fannoni 2: wato na farko, idan an yi bitar ainihin yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, za a ga yana da tushe mai inganci, kana yanayi mai armashi da yake ciki bai taba canzawa ba. Na biyu, idan an duba tarihin kasar Sin, za a ga ba a taba rasa kalubalolin da ta fuskanta ba, sai dai hakan bai hana kasar samun ci gaba a kai a kai ba.
Maganar shugaba Xi ta tunatar mana da wani bidiyo, wanda mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta watsa kan shafin yanar gizo na sada zumunta, bayan da kasar Amurka ta kaddamar da takunkumi kan kayan latironi na Chip kirar kasar Sin a kwanan nan. Cikin bidiyon, an nuna yadda sabuwar kasar Sin ta samu nasarar kirkiro sabbin fasahohi masu muhimmanci, duk da takunkumai na tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, da kasashen yamma suka saka mata, tun bayan kafuwar kasar a shekarar 1949. Inda taken bidiyon shi ne: Wanda bai samu nasarar kashe ka ba, zai sa ka samun karin ci gaba. Wannan jimla ta takaita tarihin kasar Sin na raya kanta, tare da jure dimbin wahalhalu, wanda ya zama dalilin karfin zucin kasar a fannin tinkarar kalubaloli masu alaka da siyasa da tattalin arziki na duniya. (Bello Wang)