Shugaba Bola Tinubu ya nada Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin mukaddashin Akanta Janar na kasa.
Nadin nasa ya fara aiki ne nan take bayan tafiya hutun ritayar akant Janar mai barin gado, Dakta (Mrs.) Oluwatoyin Sakirat Madein.
- Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya
- Tinubu Na Son Ganin Kowa Ya Daina Kwana Da Yunwa A Nijeriya – Minista
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata.
A matsayinsa na ma’aikacin gwamnati kuma babban darakta a ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), Mista Ogunjimi yana da fiye da shekaru 30 na gogewa a fannin sarrafa kudi a sassan ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.
Ya rike manyan mukamai da suka hada da Daraktan kudi a OAGF da daraktan kudi da asusu a ma’aikatar harkokin waje.
Shugaba Tinubu ya yabawa Akanta Janar ta Tarayya mai barin gado, Dr. Madein, bisa sadaukar da kai da ta yi ga kasa.
Bayan ta kai shekarun yin ritaya a aikin gwamnati, Dr. Madein za ta yi ritaya daga ranar 7 ga watan Maris, 2025.