Babban taron LEADERSHIP tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da aka daga zai gudana a ranar 7 ga watan Nuwamba.
A cikin wata sanarwa da LEADERSHIP ta fitar, kamfanin ya ce a yanzu za a gudanar da taron ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, 2023 a cibiyar ‘Yar’Adua da ke Abuja.
- Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar NASENI Bayan Wata 3 Da Nadinsa
- Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”
Tun da farko dai an saka ranar 3 ga Agusta a matsayin ranar gudanar da taron, amma sakamakon wasu uzuri ya sa aka dage taron.
Sanarwar ta ce, “Muna matukar godiya da goyon baya da fahimtar abokan aikinmu da wadanda za su kashe kudadensu da kuma mahalarta taron, wadanda suka himmatu wajen samun nasarar wannan muhimmin babban taro da zai kawo mafita kan ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
“Mun yi farin ciki da cewa daga karshe mun yanke ranar da za mu yi babban taron. An kuma inganta abubuwan da za su gudana a wurin taron sosai,” in ji sanarwar.
Taron mai taken, “Shaye-shayen miyagun kwayoyi, laifuka, rashin tsaro da ci gaban kasa,” abun yaba ne da shi a matsayin muhimmin matakin zamantakewa a wannan lokaci.
LEADERSHIP ta yi hadin gwiwa da hukumar NDLEA da abokan huldarta wadanda suka amince da daukar nauyin gudanar da babban taro domin bayyana illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da tasirinsa kan aikata laifuka da ci gaban kasa tare da yin nazari kan hanyoyin magance lamarin.
A binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na ta’ammuli da kwayoyi a shekarar 2017, bisa kiyasin al’ummar Nijeriya miliyan 98, ‘yan Nijeriya miliyan 14.3 ne ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi da ke illata kwakwalwa.
Baya ga shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, akwai mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma babban lauya mai fafutukar kare hakkin Bil’adama, Mista Femi Falana, da sauran su duk za su halarci babban taron.