ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron LEADERSHIP Da NDLEA Zai Gudana Ranar 7 Ga Nuwamba

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
NDLEA

Babban taron LEADERSHIP tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da aka daga zai gudana a ranar 7 ga watan Nuwamba.

A cikin wata sanarwa da LEADERSHIP ta fitar, kamfanin ya ce a yanzu za a gudanar da taron ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, 2023 a cibiyar ‘Yar’Adua da ke Abuja.

  • Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar NASENI Bayan Wata 3 Da Nadinsa
  • Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”

Tun da farko dai an saka ranar 3 ga Agusta a matsayin ranar gudanar da taron, amma sakamakon wasu uzuri ya sa aka dage taron.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce, “Muna matukar godiya da goyon baya da fahimtar abokan aikinmu da wadanda za su kashe kudadensu da kuma mahalarta taron, wadanda suka himmatu wajen samun nasarar wannan muhimmin babban taro da zai kawo mafita kan ta’ammuli da miyagun kwayoyi.

“Mun yi farin ciki da cewa daga karshe mun yanke ranar da za mu yi babban taron. An kuma inganta abubuwan da za su gudana a wurin taron sosai,” in ji sanarwar.

LABARAI MASU NASABA

NASCON Za Ta Kaddamar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Koli Na Kano

Sojoji Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Sace, Sun Kama Mutane 2 A Kaduna

Taron mai taken, “Shaye-shayen miyagun kwayoyi, laifuka, rashin tsaro da ci gaban kasa,” abun yaba ne da shi a matsayin muhimmin matakin zamantakewa a wannan lokaci.

LEADERSHIP ta yi hadin gwiwa da hukumar NDLEA da abokan huldarta wadanda suka amince da daukar nauyin gudanar da babban taro domin bayyana illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da tasirinsa kan aikata laifuka da ci gaban kasa tare da yin nazari kan hanyoyin magance lamarin.

A binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na ta’ammuli da kwayoyi a shekarar 2017, bisa kiyasin al’ummar Nijeriya miliyan 98, ‘yan Nijeriya miliyan 14.3 ne ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi da ke illata kwakwalwa.

Baya ga shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, akwai mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma babban lauya mai fafutukar kare hakkin Bil’adama, Mista Femi Falana, da sauran su duk za su halarci babban taron.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
     2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NASCON Za Ta Kaddamar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Koli Na Kano
Labarai

NASCON Za Ta Kaddamar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Koli Na Kano

November 26, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Sace, Sun Kama Mutane 2 A Kaduna
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Sace, Sun Kama Mutane 2 A Kaduna

November 26, 2026
Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Zargin Cin Zarafi Da Sarkin Daura Ya Yi Wa Wata Baturiya
Manyan Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Zargin Cin Zarafi Da Sarkin Daura Ya Yi Wa Wata Baturiya

November 26, 2026
Next Post
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi

An Cafke Mutum 23 Bisa Zargin Aikata Zamba Ta Intanet A Sakkwato

LABARAI MASU NASABA

NASCON Za Ta Kaddamar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Koli Na Kano

NASCON Za Ta Kaddamar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Koli Na Kano

November 26, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Sace, Sun Kama Mutane 2 A Kaduna

Sojoji Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Sace, Sun Kama Mutane 2 A Kaduna

November 26, 2026
Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Zargin Cin Zarafi Da Sarkin Daura Ya Yi Wa Wata Baturiya

Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Zargin Cin Zarafi Da Sarkin Daura Ya Yi Wa Wata Baturiya

November 26, 2026
INEC Ta Ce Yanzu Masu Rijistar Zaɓe Sun Haura Miliyan 100 A Nijeriya

INEC Ta Ce Yanzu Masu Rijistar Zaɓe Sun Haura Miliyan 100 A Nijeriya

November 26, 2026
’Yan Daba Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Da Ofishin Jam’iyyarsa Hari A Edo

’Yan Daba Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Da Ofishin Jam’iyyarsa Hari A Edo

November 26, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

Gwamnatin Kano Na Shirin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje

November 26, 2026
Gwamnan Kano Ya Koma APC Ba Tare Da Wani Ya Tilasta Masa Ba – NDC

Gwamnan Kano Ya Koma APC Ba Tare Da Wani Ya Tilasta Masa Ba – NDC

November 26, 2026
Kwankwaso Bai Je Ƙasar Waje Neman Magani Ba – Kwankwasiyya

EFCC Za Ta Duba Ƙorafi Kan Gidaje Da Ake Zargin Suna Da Alaƙa da Kwankwaso

November 26, 2026
’Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 30 A Harin Ramuwar Gayya A Neja

’Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 30 A Harin Ramuwar Gayya A Neja

November 26, 2026
Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ƙara Kai Wa ’Yan Ta’addan Hari Domin Murƙushe Su

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ƙara Kai Wa ’Yan Ta’addan Hari Domin Murƙushe Su

November 26, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.