Ra’ayoyin da aka gabatar a taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC), da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar (CPPCC), ciki har da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da neman ci gaba mai inganci, da zurfafa yin kwaskwarima da ma kara fadada bude kofa ga kasashen waje bisa wani matsayi mai karin inganci, wadanda suka jawo hankulan al’ummun kasashe daban daban.
Wasu ‘yan kasashen waje sun bayyana cewa, tarukan biyu na kasar Sin sun nuna amincewar kasar ta fuskantar kalubale da sa kaimi wajen neman ci gaba, kana sun bayyana yadda kasar Sin ke more damar ci gaba tare da kasa da kasa, da ma yin aiki kafada da kafada tare da kasashen duniya.
- Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer
- Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer
Tsohon firaministan kasar Belgium Yves Leterme ya ce, ra’ayin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko yana da kyau matuka, wadanda suka kasance babban ci gaba ne da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki.
Wasu kuma sun bayyana cewa, ra’ayoyin ci gaba na kasar Sin sun jaddada muhimmancin raya kasa cikin lumana, da samun moriyar juna da kuma cimma nasara tare, suna kuma fatan kara gudanar da hadin gwiwa tare da kasar.
Tsohon ministan tattalin arziki da kudi na kasar Italiya Giovanni Tria ya ce, yana matukar kulawa da manufofin tattalin arzikin kasar Sin, kuma Sin za ta taka rawar gani a harkokin cinikayyar kasa da kasa, da bude kasuwanni, da samar da sauki ga mutanen kasashen waje wadanda ke neman zuba jari kan masana’antun kasar. A cewarsa, kasuwar kasar Sin na cike da damammaki ga jarin waje.
A nasa bangaren, tsohon firaministan kasar Iraki Adil Abdul-Mahdi ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin bai kwaikwayi tsarin wasu kasashe ba, haka kuma bai mamaye sararin ci gaba na sauran kasashe ba. Zamanintarwa irin ta kasar Sin na kokarta tabbatar da cigaba irin na samun moriya tare a zahiri. (Mai fassara: Bilkisu Xin)