Kakakin hukumar ayyukan ‘yan sama jannati ta kasar Sin Lin Xiqiang, ya ce tashar binciken samaniya ta Sin wato Tiangong, za ta ba da damar cimma manyan nasarori a fannin binciken kimiyya, da bangarorin kirkire kirkire a nan gaba.
Lin Xiqiang, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, ya kara da cewa, tashar Tiangong ta shiga sabon mataki na aiwatar da manufofi, da samar da ci gaba, wadanda za su gudana cikin tsawon sama da shekaru 10, tun bayan kammalar ta a shekarar 2022.
Lin ya kara da cewa, akwai fatan cewa wannan tasha, za ta haifar da nasarori a sassan binciken kimiyya mai nasaba da binciken asalin duniyoyi, da hallitu marasa haske dake sararin samaniya, da karfin maganadisun su, da dandazon taurari, da nau’o’in haske, da rukunin duniyoyi da taurari masu makwaftaka, da yadda taurari ke faruwa da sauyawar su, da ma yanayin duniyoyin da ke wajen falakin rana.
Jami’in ya kara da cewa, burin da ake da shi game da bincike a wannan tasha shi ne gano asali, da yanayin sauyawar duniyoyi, da yanayin faruwar halittu, da ma yiwuwar dan Adam ya rayu tsawon lokaci a samaniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)