ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 hours ago
Hainan

Da safiyar ranar 18 ga wata,babban darektan kamfanin Wenye (Hainan) na sarrafa kayayyakin dangogin gyada na Afirka, Luo Lingsong ya yi albishirin cewa, rukunin farko na kayayyakin dangogin gyada ya samu iznin kwastam na shiga kasuwar babban yankin kasar Sin, bayan da aka fara aiki da tsarin kwastam na musamman a tashar teku ta ciniki mai ’yanci da ke tsibirin Hainan.

Lallai a wannan rana, a hukumance ne aka fara aiwatar da tsarin kwastam na musamman a tashar teku ta ciniki mai ’yanci da ke lardin Hainan na kudancin kasar Sin, kuma daga cikin rukunin kayayyaki na farko da suka ci gajiyar sabon tsarin, akwai kayayyakin dangogin gyada da nauyinsu ya kai tan 10 na kamfanin Wenye, wadanda aka sarrafa da ‘ya’yan Macadamia na Kenya da Yazawa na Tanzania da ma ‘ya’yan Pecan na Afirka ta kudu, wadanda kuma aka tura su zuwa lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin.

Hakan ba kawai ya alamanta yadda aka fara aiki da tsarin kwastam na musamman a tashar teku ta ciniki mai ’yanci ta Hainan ba ne, har ma ya bude sabon babin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Bayan da aka fara daukar wannan sabon tsarin na kwastam na musamman, an fadada nau’o’in kayayyakin da aka cire musu harajin kwastam daga sama da 1900 har zuwa sama da 6600, wanda hakan ya samar da alfanu ga kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa. Kamar yadda jakadan kasar Afirka ta Kudu a kasar Sin Siyabonga C. Cwele ya bayyana a baya cewa, “Matakai na nuna gata da za a dauka a tashar teku ta ciniki mai ’yanci da ke tsibirin Hainan, sun taimaka wa kasashe masu tasowa yalwaita kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasar Sin har da daga darajar kayayyakinsu, sakamakon yadda aka rage ko cire musu harajin kwastam.” Ga shi yanzu, matakan na samar da damammaki na hakika ga kasashen.

ADVERTISEMENT

Bisa ga tsarin kwastam na musamman da aka dauka a tashar, baya ga yadda aka cire harajin kwastam a kan kayayyakin da aka shigo da su daga ketare, an kuma dauki mataki na cire harajin kwastam a kan kayayyakin da ake sayarwa daga tashar zuwa babban yankin kasar Sin, muddin darajarsu ta karu da sama da kaso 30% bayan sarrafa su a tashar, kuma hakan ya samar da kyawawan damammaki ga masana’antun sarrafa kayayyaki.

Bari mu ba ku misali da kamfanin Wenye(Hainan) na sarrafa kayayyakin dangogin gyada na Afirka, kamfanin ya shigo da dangogin gyada daga Kenya da Tanzania da kuma Afirka Hainan ba tare da biyan harajin kwastam ba, kuma bayan da ya sarrafa dangogin gyada zuwa kayayyaki iri iri wadanda darajarsu ta karu da sama da kaso 30%, ya iya sayar da su zuwa kasuwar babban yankin kasar Sin ba tare da biyan harajin kwastam ba. Ta wannan tsari ne za a daga darajar kayayyakin Afirka, tare da kara kudin shigar manoman Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamban bana, kudin ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 314 da miliyan 413, adadin da ya zarce dala biliyan 300 a karon farko, kuma ya karu da kaso 17.8% in mun kwatanta da na makamancin lokacin bara, har ma ya zarce na gaba dayan kudin cinikin na shekarar 2024, wanda ya kai dala biliyan 295 da miliyan 562. Nau’o’in kayayyakin kasashen Afirka na shigowa kasuwar kasar Sin, ciki har da yazawa na Nijeriya da ‘ya’yan Cocoa na Kamaru, da vanilla na Madagarscar da ‘ya‘yan kofi na Habasha da auduga na kasashen yammacin Afirka da sauransu. Bayan da aka fara aiki da tsarin kwastam na musamman a Hainan, to, tabbas karin kayayyaki daga kasashen Afirka za su samu saukin shigowa kasuwar kasar Sin. Baya ga haka, tuni aka raba nasarorin kirkire-kirkiren da aka samu a cibiyar renon ire-iren shuka ta Nanfan da ke lardin Hainan ga kasashen Afirka irinsu Senegal da Tanzania, ta shirye-shiryen da aka aiwatar bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, a kokarin samar da wadataccen abinci da inganta ayyukan gona a kasashen. Ta hakan kuma, za a kai ga inganta hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka daga cinikin da aka saba yi har zuwa fannonin raba fasahohi da hadin gwiwar masana’antu, don su kara cin moriyar juna.

A hakika, tashar teku ta ciniki mai ’yanci da ke tsibirin Hainan ba kawai ta kasance sabon dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ba ce, a’a, har tana sa kaimi ga kasa da kasa wajen bude kofa da hada gwiwa da juna. Kamar dai yadda Bernard Momanyi, dan jaridar kasar Kenya ya fada, “Yadda aka fara aiki da tsarin kwastam na musamman a Hainan ba kawai yana da muhimmanci ga kasar Sin ba, hatta ma ga duniya baki daya, sakamakon yadda hakan zai inganta bude kofar kasar Sin ga duniya da yalwaita ciniki a tsakanin kasa da kasa da sa kaimin kafa tattalin arzikin duniya mai budadden salo, kuma duniya baki daya za ta amfana.”

Lallai bisa bunkasar tashar teku ta ciniki mai ’yanci ta Hainan, Sin da kasashen Afirka za su kara karfafa hadin gwiwarsu, kuma ciniki da tattalin arzikin duniya za su kara bunkasa. Karin kayayyaki masu inganci na Afirka za su samu saukin shigowa kasuwar kasar Sin bisa tashar nan ta Hainan, a sa’in da za a kara samar wa kasashen Afirka masana’antu da fasahohi na kasar Sin da suke matukar bukata. Sin da kasashen Afirka za su ci moriyar juna bisa ga yadda suka bude kofa ga juna, tare da tinkarar kalubalen da ke gabansu ta hanyar hadin gwiwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

December 17, 2025
Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

December 16, 2025
Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI
Ra'ayi Riga

Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI

December 15, 2025
Next Post
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.