Kayayyakin da aka yi jigilarsu a sashen dakon kaya na tashar tekun Ningbo-Zhoushan da ke lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, sun zarce tan biliyan 1.37 a shekarar 2024, inda hakan ya sa tashar ta sake zama kan gaba a duniya karo na 16 a jere.
Adadin kwantenonin da aka yi hada-hadarsu a tashar ya kai miliyan 39.3 a bara, inda ya karu da kashi 11 cikin 100 a shekarar, wanda ke nuna an samu ci gaba mafi girma da ba a ga irinsa cikin shekaru bakwai da suka gabata ba.
Tashar tekun ta Ningbo-Zhoushan tana da hanyoyin kwantena fiye da 300, gami da hanyoyin kasa da kasa sama da 250, tare da sada tasoshin teku sama da 600 a cikin kasashe da yankuna fiye da 200. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)