Cibiyar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta kasar Sin ko CDC, ta ce adadin mutane dake kamuwa, da masu rasuwa sakamakon harbuwa da cutar HIV mai karya garkuwar jiki a kasar ya yi matukar raguwa, zuwa matsayi mafi kankanta a dukkanin duniya.
Alkaluman CDCn sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2022, Sin na da jimillar mutane kusan miliyan 1.22 dake dauke da cutar ta HIV ko AIDS, kana adadin wadanda cutar ta hallaka tun bullarta a kasar a shekarar 1985 zuwa yanzu ya kai mutum 418,000.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Raya Yankin Delta Na Kogin Yangtze
- Sin Ta Kammala Tsara Aikin Tauraron Dan Adam Mai Nisa Na Farko Domin Samar Da Hidimar Intanet Mai Inganci
Cibiyar ta ce bayan aiki tukuru, tsarin kasar Sin na kandagarki da shawo kan cututtuka masu yaduwa ya inganta, kana ikon kasar na dakile bazuwar su shi ma ya kyautata. Kaza lika Sin ta kafa tsarin ba da magunguna, da jinyar masu dauke da cutar, wanda ya karade gundumomin kasar 2,517. Bugu da kari, kaso sama da 90 bisa dari na masu dauke da cutar HIV a kasar na karbar magungunan rage tasirinta, yayin da kaso sama da 95 bisa dari suka cimma nasarar dakile tasirin cutar a jiki su.
Tun daga shekarar 2004, Sin ta kafa manufofin tallafawa mutanen dake dauke da wannan cuta da ma iyalansu, ciki har da samar musu da magunguna, da tallafin rayuwa. Har ila yau, marayun wadanda cutar ta hallaka na samu ilimi kyauta. Yau Juma’a, 1 ga watan Disamba ce ranar cutar AIDS ta duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp