• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tasirin Karancin Kudade Ga Kananan Sana’o’i

by Hussaini Najidda Umar
3 years ago
Kananan sana’o'i

Shin wannan matsala da ‘yan Nijeriya suka shiga ta hada-hadar kudade tana shafar kananan sana’oi ko kawai masu mnayan kudade ne suke shan wahala? A ‘yan kwanakin nan babu abin da ludayinsa ke kan dawo irin tsarin sauya launin kudade a Nijeriya.

Kamar yadda kowa ya sani ne babban bankin Nijeriya wato CBN ya sauya launin takardun kudi wato takardar Naira 1000 da Naira 500 da 200. Kafin zuwa karshen watan Janairu duk ‘yan Nijeriya masu wadancan kudade sun garzaya bankuna don kai tsoffin kudade don musanyasu da sababbi.

  • Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi

Kowa na sane da yadda mutane suka shiga halin dimuwa da wahala wajen sauya takardun kudaden nasu. Sannan kuma yadda jama’ar Nijeriya suka dimauce ta neman kudade a hannu shima wani hali ne da ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu inda takardun kudi musamman sababbin suka zama kamar wasu gwalagwalai.

A ranar Lahadin karshen watan Janairun wannan shekarar Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa ‘yan Nijeriya kwanaki goma don su ci gaba da sauran tsoffin kudaden da suke rage a hannunsu. Saboda kiraye kiraye da shugabanni suka yin a neman an janye shirin zuwa wani lokaci.

Majalisar dokokin kasa ta dattijai da ta wakilai suma sunyin nasun kokarin wajen jawo hankalin babban bankin Nijeriya don ya sauya tunani, wajen sauya launin kudin. A haka ne ita majalisar wakilai ta yi wani kudiri inda ta nemi tsarin sauya fasalin kudin ya kai watan Yulin wannan shekarar don bai wa ‘yan Nijeriya damar canja kudadensu don gudun asara.

LABARAI MASU NASABA

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

Hakika wannan tsari na babban bankin Nijeriya ya zo wa da ‘yan Nijeriya wata sabuwar wahala wacce har yanzu take yi wa ‘yan Nijeriyar barazana na hana su yin kasuwanci cikin jin dadi da annashuwa.

Kowa na tare da sanin cewa bankunan kasuwanci na Nijeriya sun taka muhimmiyar gudunmawa wajen kuma ta’azzara wannan wahala ga ‘yan Nijeriya.

Har ila yau wannan tsarin na babban bankin Nijeriya kamar yadda wasu masana tattalin arziki suka fada sun ce ba zai yi wa masu kananan sana’oi dadi ba musamman wadanda suka dogara kacokan wajen hulda da kudade a fili. Misali kowa ya sani cewa ‘yan kasuwa da suke sayar da abubuwan amfanin yau da kullum kamar kayan abinci da sauran kananan abubuwa wadanda sai dasu mutane suke samu suyi amfani da su don cin abinci. Kamar kayan miya da man girki da ake auna wa kadan-kadan akan karamin farashi da suaransu.

Irin wadannan sana’oi hakika da yawan ‘yan Nijeriya wadannan sana’o’in da su suka dogara. Saboda haka a wannan hali da ake cikin yanzu su irin wadannan kasuwanci su ne suke shan bugu saboda karancin kudade da yake hannun mutane. Sannan kuma kamar yadda na dada a baya su dai wadannan sana’oi yawanci masu yinsu ba su da asusun banki.

Ta haka ne ya sa da yawansu suke shan wahala wajen yin ta’ammali da mutane. Kamar yadda na ga wata mace a mota tazo tana sayen doya a wajen wani mai sayar da doyar bayan ta gama ciniki sai ta fadawa mai doya ya bata lamabar asusu za ta tura masa, a nan me doya ya ce ai shi sam bai san zance ba.

Haka matar nan tana ji tana gani ta hakura ta bashi doyarsa. Anan hakika wannan me doya ya yi rashin wannan ciniki saboda kawai ba shi da lambar akawunt na banki ko nace bashi da asusun banki.

Mutane da yawa ‘yan Nijeriya masu kananan sana’oi hakika suna da kalubale na mallakar asusun banki, saboda yadda su kansu bankunan ba sa samar da tsari me kyau wanda zai sa ‘yan Nijeriya su yi hulda da su. Kowa na sane da yadda yanzu shi kansa yadda aikin sabis na intanet ya ke wahalar da mutane wajen tura kudade zuwa asusun jama’a. Musanman lokacin da aka fara wannan aiki na sauya launin kudade.

Kananan sana’oi a kasashen da suka damu da ‘yan kasar suna yin tsari me kyau ta yadda duk wasu tsare tsare da aka kirkira a cikin kasa suna bawa ‘yan kasar dama ta yadda ba za su sha wahala ba ko kadan bayan samar da tsare-tsare.

A nan ya zama dole ga gwamnatocinmu su rika saka ‘yan kasa a cikin tsare-tsarensu a duk lokacin da suka fito da wani sabon tsari don saukakawa ‘yan kasar. Kananan sana’o’i a duk kasashen duniya su ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki, duk sanda aka samu matsala wajen kula da wadannan sana’o’i to hakika jama’a da yawa za su ji jiki, kamar yadda yanzu ‘yan Nijeriya suke gani.

Sannan kuma ya zama dole muma ‘yan Nijeriya mu dawo daga tunani irin na da, domin rungumar ci gaba da duniyar fasaha take zuwa da su.

Ya zama dole ga jama’a da su bude asusun ajiya a bankuna domin taimakon kasuwancinsu da kuma bai wa kudadensu tsaro mai inganci. Har’ila yau suma bankunan dole su samar da tsaro da karfin fasaha wajen kare dukiyoyin jama’a da don rungumar wannan tsarin na takaita amfani da kudade a fili.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Next Post
Duk Wanda Zai Yi Noma Ya Tabbatar Da Kiyaye Lokaci – AFAN

Duk Wanda Zai Yi Noma Ya Tabbatar Da Kiyaye Lokaci - AFAN

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

October 11, 2025
Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

October 11, 2025
Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

October 11, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

October 11, 2025
Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

October 11, 2025
An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

October 11, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.