A makon jiya ne dai cacar-baki ta barke tsakanin Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da matsalar fatara da yunwa da ke karuwa a Nijeriya.
LEADERSHIP Hausa ta dai yi tilawar cewa a kwanakin baya ne Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da wani rahoton da ke cewa ‘yan Nijeriya miliyan 133 ke fama da talauci.
Biyo bayan wannan rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya fito bayyanar jama’a ya zargi gwamnonin kasar nan da karkatar da kudaden kananan hukumomi gami da karkatar da kaso 13 na jihohin da ake hakar mai a cikinsu, batun dai ya fusta gwamnoni matuka.
Kazalika, zargin na Buhari na zuwa ne bayan da karamin ministan kasafi da tsare-tsare, Clement Agba, ya yi zargi makamancin wannan da cewa gwamnonin sun kasa zuba kudaden da suka dace ga al’ummomin kauyuka wanda hakan ya jawo cigaba bai samu shiga har kauyuka ba balle a fitar da yawansu daga cikin talauci.
Sai dai kuma, kungiyar gwamnonin Nijeriya ta fito ta maida martani kan wannan batun, kodayake a fakaice ba su ambaci sunan Shugaba Buhari kai tsaye ba, sai suka fake suka dira kan karamin ministan kasafin, suna masu cewa gwamnatin tarayya ce ke da alhakin hauhawar matsalar farata.
A wata sanarwar da kakakin kungiyar NGF, Abdulrazakue Bello- Barkindo, ya fitar, gwamnonin sun zargi Shugaba Buhari da gazawa wajen kare manoma daga hare-haren ‘yan bindiga dadi tare da jagorantar gwamnati a yanayin da kamfanin NNPC ya ki tura kudade ga asusun gwamnatin tarayya na tsawon watanni.
Gwamnonin suka ce, kwata-kwata bayanan ministan ba daidai ba ne, a kan hakan ma, suka ce, gwamnatin tarayya ta mance da asalin nauyin da ke rataye a wuyanta na kare al’ummar kasa, inda suka misalta hakan a matsayin kokarin karkatar da hankali daga asalin gazawar gwamnatin tarayya.
Gwamnonin dai sun kara da cewa ta’azzarar matsalar tsaro da ya addabi yankunan karkara shi ne musabbibin abun da ya hana su zuwa gonaki don yin noma kuma hakan ne ya janyo talauci ya musu katutu. Don haka ne suka misalta matsalar da cewa kawai na faruwa ne a sakamakon gazawar gwamnati na samar da wadataccen tsaro ga al’ummar kasa.
Kan hakan ne LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Shehin malami kuma masani a bangaren tattalin arziki (Economy), Farfesa Ahmad Sanda, da ke aiki a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto a tsangayar nazarin tattalin arziki kuma tun da ya fara a aiki a jami’ar 1987 har zuwa yanzu yana koyarwa ne a tsangayar nazarin tattalin arziki, ya tabbatar da cewa, dukkanin bangarorin biyu na gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi na da rawar da za su taka wajen fitar da al’ummomi daga talauci, don haka ne ya ce kowa na da nakasu a bangarensa.
Ya ce, akwai kamshin gaskiya na cewa Gwamnoni sun taka rawa wajen asasasa talauci a kasar nan musamman a arewacin Nijeriya.
Farfesa Sanda ya ce, a zahiri, farko idan ana maganar matsalar tattalin arziki abu na farko da za a fara dubawa shi ne matsalar tsaro da ya addabi kasar nan, yana mai cewa matsalar tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen gurgunta al’umma musamman na karkara lura da cewa dubban jama’a basa iya noma sakamakon fargabar matsalar tsaro ko kuma korarsu daga yankunan da suke. Ya misalta noma a matsayin hanya da ke matukar taimaka wa tattalin arzikin kasar nan.
Ya ce, duk kasar da ya zama akwai matsalar kiwon lafiya, noma, tsaro to kuwa kasar na cikin matsalar da za ta sha wuya wajen shawo kan matsalar fatara da talauci, ya nuna cewa dole ne sai an duba wadannan matsalolin an musu gyara kafin tukunna a yi batun fita daga cikin matsalar talauci.
Shehin malamin a bangaren nazarin tattalin arzikin na cewa: “Muna iya kallonshi ta hanyoyi daban-daban. Hanya ta farko, da yake ka san akwai matsalar tsaro, an san cewa ita gwamnatin tarayya ita take da karfin dakile matsalar tsaro fiye da jihohi, amma mutane a matakin kananan hukumomi da gwamnatin jiha su suka san wurare, saboda haka da a ce su Gwamnonin Nijeriya sun himmatu wajen shawo kan wannan matsalar da tabbas an samu raguwar matsalar musamman a Arewa.
“Sannan za ka zo ka duba bangaren ilimi, inka duba makarantun nan musamman, a Firamare da Sakandari kowa ya san iri matsalolin da ake fuskanta.
Albashin Malamai a halin yanzu abun in ka ji shi sai ga ya kai fagen sai lahaulla waalaakuwata, saboda a halin da ake ciki za ka iya tarar da malami a Firamare wanda albashinsa bai taka kara ya karya ba. Da yawansu akwai wadanda suke karbar albashi kasa da dubu goma, saboda Allah idan an ce ana son ci gaba ta yaya da irin wannan yanayin na hauhawar farashin kayayyaki ta yaya za a bai wa malami dubu goma a ce kuma ya je ya yi aiki?
Ko shi kadai kuma a ce bai da iyalai ai dubu goma ya kasa masa masa kwarai da gaske ballanta ma yanzu abin akwai ban tausayi irin yadda muka ga kanmu a ciki ta bangaren ilimi.
“Mu dawo bangaren noma, shi ma akwai matsaloli da dama. Farashin Takin zamani na hauhawa a cikin ‘yan shekarun nan, yanzu manoma da dama ba su iya sayen Taki su zo su bunkasa nomansu a nan yankin arewa.
To, gaskiya matsaloli ne masu yawa da gwamnonin nan sun maida hankula sosai suka fuskanci yadda wadannan abubuwan suke da gaskiya za a samu sauki na matsalar da ya shafi talauci musamman a arewacin Nijeriya, amma ka ga abun ya ta’azzara domin sun kasa taka rawar da ya kamata su taka.”
Farfesa Umar Sanda, ya ce, a zahirin gaskiya duk da yake dai ita gwamnatin tarayya tana da rawar da za ta taka sosai mai karfi na farfado da tattalin arziki, amma ya kamata su ma gwamnonin su himmatu s daura damarar ganin sun farfado da tattalin arzikin yankunansu.
“Sannan ka ga akwai maganar kiwon lafiya nan ma akwai matsaloli idan ka je asibiti za ka ga irin matsalolin da suke jigbe.”
Dangane da alkawuran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewa zai fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga cikin kangin talauci, ya ce nauyin fitar da jama’a daga cikin kangin talauci ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya data jihohi dukkaninsu, amma duk da hakan gwamnatocin jihohi sun fi kusa da jama’a don haka sune suka fi dacewa su yi abubuwan da suka kamata domin samun mafita.
Ya kara cewa: “Gwamnatin jihohi su za su fi daukan laifin wannan matsalar saboda suke tare da jama’a in ma ka dubi yadda gwamnatin Shugaba Buhari babu wani lokacin da ba a tura wa jihohi da kananan hukumomi kudadensu ba. To amma ka ga gwamnonin Nijeriya baki daya sun yi shuri da maganar cewa a bai wa kananan hukumomi kasonsu kai tsaye da za su iya gudanar da abubuwansu a kashin kansu, sai suka kirkiro wannan matsalar ta ‘Joint account’.
Suka hana kananan hukumomi su samu ‘yancin kashin ta bangaren samun kasonsu kai tsaye daga gwamnatin tarayya, a kan haka nan sai ka ga in ka je karamar hukuma babu wani aikin da ake gudana illa kawai dai a raba albashi a watse shi kenan, amma ba ka ganin wani aiki, kuma mutanen nan su ke tare da talakawa, sune suka san matsalolinsu suke tare dasu, su ya kamata a ce su za a fara tuntuba idan wata matsala ta samu ko su ya kamata ana hangen wata matsala su za a fara tuntuba to basu da wannan sukuni na su fito da kudi su tunkari matsaloli da ke fuskantar talakawansu.”
Ya ce, tabbas idan ana son a samu cigaba lallai ya kamata a ce kananan hukumomi suna da nasu kason kai tsaye daga gwamnatin tarayya.
Farfesa Sanda, yana mai cewa a duk lokacin da talauci ya addabi mutanen kauyuka sukan fito cikin birane domin neman saukin rayuwa wanda hakan ma wani karin matsaloli ne ga tattalin arzikin kasar nan.
“Tun da dadewa wannan matsalar ta fara kunno kai mutane suna dawowa birni, yanzu kuma abubuwan sun kara ta’azzara saboda matsalolin tsaro da na tattalin arziki.”
Ya ce, da zarar aka shawo kan matsalolin da suka sanya jama’a fitowa daga kauyukansu za su koma domin cigaba da rayuwa, yana mai cewa da zarar aka kawo karshen matsalar tsaro da na kuncin rayuwa a kauyuka wannan matsalar za ta zama tarihi.
“Amma idan jama’a suka cigaba da dawowa cikin birane ka ga za a fuskanci wasu matsalolin kuma kenan. Na farko ka ga shi kanshi tattalin arzikin arewa da ya dogara a kan noma zai samu matsala saboda idan masu noman suka shigo birni su waye za su yi aikin noma su ciyar da jama’a?
sannan idan mutane na dawowa birni makarantu za su yi karanci, asibitoci za su samu yawa fiye da yadda aka tsara da sauran bangarori don haka da birni da kauyukan dukka za a samu matsala sakamakon komawar mutanen kauye zuwa birni muddin in ya ci gaba.”
Farfesan ya ce, dole ne fa sai an dauki matakan da suka dace na hikimomi da dabaru domin ganin an shawo kan matsalolin talauci ba wai tsayawa ana cacar baka a tsakanin bangarorin biyu ba.
Ahmad Sanda ya kuma ce akwai alfanu da rashin alfanu na shiga kauyuka da masu hannu da shuni ke yi na saye amfanin gona da kuma saye amfanin gona ko kuma daukan hanyar mutanen kauye don su yi masu noma.
“Masana tattalin arziki na cewa idan ana yin noma mai dumbin yawa ana sa ran cewa za a samu wasu alfanu, ana sa ran wanda ke da babban gona zai fi iya samun kuzarin noma kowani buhu, misali in buhun shinkafa ne zai iya noma shi a kan farashi kasa da wanda in mai karamin karfi ne zai yi. Sannan kuma wadanda suke da manyan gonanaki tana yiyuwa suna iya samun tallafi daga bankuna don su yi abubuwan da suke bukata don bunkasa nomansu. Amma wanda yake da karamin karfi zai iya yiyuwa ba zai samu irin wannan damar ba.
“Sai dai kuma matsalolin da za su iya biyo bayan irin wannan za a samu karancin abinci ke nan. Idan har manomin da ke kauye zai fito ya je ya yi noman kudi ga mai babban karfi zai zama kenan shi ya bar nasa noman ya je yin na wani kuma, hakan zai sanya talauci ya shigo ko mutum ya wayi gari bai da karfin tattalin arzkin abincin da zai iya ciyar da iyalansa.
“Hanyoyin da za a iya bi a tabbatar an kalli matsalolin da su mutanen da ke karkara ke fuskanta, misali matsalar Taki, da shekarun baya ai gwamnatocin jihohi a arewa suna sayen Taki suna bada tallafi ana amfani da shi wajen noma. Ka ga idan za a farfado da irin wadannan abubuwan za a cigaba da su manomi zai iya samun dama ya noma abin da zai iya ciyar da iyalinsa har ma da wanda zai sayar.”
Umar Sanda ya kuma ce, baya ga wannan, akwai wani barazanar da ake fuskanta wanda zai iya kara ta’azzara lamura muddin ba a dauki matakan da suka dace ba, ya ce wasu kasashe suna fama da matsalar sauyin yanayi, don haka da bukatar Nijeriya ta yi hankali don kauce wa irin wannan.
“Sannan akwai maganar sauyin yanayi wanda a halin yanzu wasu kasashe sun fuskanci fari mai radadi kusan shekara biyu zuwa hudu, ya kamata idan an hangi fari daga kasashen yammacin Afrika ya kamata ya zamana a ce an fito da wani tsari na bada wasu ire-iren shuka wadanda za su sa manoma su shuka su girbe koda an samu karancin ruwa, kenan akwai bukatar a samar da ire-ire wadatattu, sannan a samu malaman gona wadanda za su iya gwada musu ga yadda za a yi a yi aiki da irin wadanna sabbin Irarruka.
“Na san wasu jami’o’i a nan Arewacin Nijeriya sun taka rawa sosai ga wannan fannin, musamman Jami’ar ABU Zariya ka ga suna da cibiyar bincike inda suke fitowa da Irin Shuka masu inganci.
“Matsalar da ke nan shi ne can da muna da malaman gona, amma yanzu kwata-kwata babu su, babu malaman gona, ta yaya za a iya farfado da tattalin arzikin manomi shi ne a tabbatar da cewa wadannan matsalolin da yake fuskanta an shawo kansu. A samar musu da malaman gona da za su nuna musu yadda za su yi amfani da ire-iren wanda koda an samu fari hakan zai taimaka.
“Sannan sai bangaren banki manomanmu sai ka tarar ba ma su da asusun ajiya a banki balle ma su iya samun tallafi ta hanyoyin da ya kamata domin su inganta nomansu. Idan manoma ya kasance bai da asusun ajiya a banki kuma bai da wata kungiya da za ta taimakeshi wajen samun tallafi daga bankuna ka ga wadannan ma matsala ne. Don haka wadannan abubuwan ya kamata a kallesu da idon basira a tsara karfafa wa manoma don ganin an samu mafitar farfado da tattalin arzikin kasar nan,” a cewar Farfesa.
Ita dai kungiyar gwamnonin Nijeriya ta ce, kamatuwa ya yi karamin ministan kasafin ya kalubalanci ministar kudi dangane da yadda suka jefa al’ummar kasa cikin fatara da talauci ba wai ya maida hankali wajen sukar gwamnonin ba.
“Zarge-zargen ministan a kanmu gaba daya babu gaskiya a ciki domin kuwa sune suka gaza wajen shawo kan matsalar tsaro wanda hakan ya kara ta’azzara lamura inda tattalin arzikin jama’a ya kara shiga cikin mawuyacin hali.”
“Aikin farko na kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyar jama’a. gwamnatin tarayya da alhakin kare rayuka da dukiyar jama’a ya rataya a wuyanta ta kasa shawo kan matsalar garkuwa da mutane, kashe-kashe, aikace-aikacen ‘yan bindiga, da sauransu.”
Kazalika, wakilinmu Hussaini Yero, Gusau ya nemi fashin baki a wajen shugaban tsangayar tattalin arziki na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau, Dakta Mustapha M. Abdullahi Kanoma, inda ya bayyana cewa, hukumar kididdiga tana da ma’auni da take aiki da shi wajen bincike gani abubuwa.
“Akwai ma’auni guda uku da na sani. Wadannan ma’aunan uku su na da rassa goma. Guda ukun su ne bangaren ilimi, lafiya da bangaren inganta rayuwa. A bangaren lafiya ya kunshi abinci mai gina jiki (Nutrition) da adadin yaran dake mutuwa (Child mortality). A bangaren ilmi kuwa shekarun karatu da adadin wadanda suke zuwa makaranta.
Sai na ukun shi ne inganta rayuwa. Shi wannan ingancin rayuwa tana kunshe da rassa shida. Na farko shi ne makamashin da ake amfani da shi wajen yin girki misali (itace ne ko kuma gas ko Gawayi da sauransu). Na biyu shi ne tsaftar muhalli (Sanitation) Misali irin abubuwan da ake amfani da su wajen tsaftace muhalli za ka ga wuraren da taulauci ya yi yawa ba tsafta.
“Na uku ruwan sha shi ma ana duba yanayin ruwan.
Sai na hudu wutar lantarki. Sai na biyar, gidaje, misali irin yanayi gidajen da mutane ke rayuwa ciki. Sai na shida, kadarori, shi ne adadin kadarorin da mutane suka mallaka, sun kuma hada da abubuwan hawa irin su mota, mashin wayar salula, kwamfuta, rediyo, talabijin da dai sauran su. Wadannan sune ma’aunan da hukumar ke amfani da su ta gano jihohin da suka fi talauci da fatara da ya fi yawa.
“Yanzu misali kiddidiga ta nuna yara miliyan goma ba su zuwa makaranta wanda arewa na da kaso mafi tsoka.
“Sannan ga matsalar tsaro ‘yan ta’adda sun hana manoma noma ka ga za a samu karancin abincin da kuma aikin yi wanda sanadiyar haka talauci zai karo, sai matsalar ingantaciyar lafiya saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin tsaftar muhalli zai kawo karuwar cuttutuka da mace-mace musamman na yara kanana.”
Daktan ya kara da cewa, “Sannan za ka ga a arewa muna da karancin ababen more rayuwa misali ire-irensu talabishin, babura kekuna, na’ura mai kwakwalwa (computer) fa sauran su.”
Dangane da hanyoyin da za a bi wajen magance wadannan matsalalolin ya ce, “Na farko kamar bangaren ilimi a tilasta iyaye su kai yaransu makaranta, gwamnati ta inganta makarantu sai na biyu shi ne kamar bangaren lafiya gwamnati ta inganta bangaren lafiya ta hanyar samar da kayan aiki ingantattu da ma’aikata da kuma wadatattun asibitoci a birane da karkara.”
“Gwamnati ta samar da ayyukan yi ta hanyar farfado da masana’antu da kuma kirkiro da sabbin ayyukan yi, bankuna su samarwa masu kananan masana’antu tallafi (bashi) don su habbaka sana’o’insu da wannan za a samu maganin matsalar fatara da talauci har da tsaro idan har aka samar da ayyukan yi.”
Ya ce, idan har gwamnati ta bi wadannan shawarwari za a samu raguwar talauci a jihohin kasar nan.