Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata.
Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu na bana, masana’antar samar da kayayyaki na samun saurin bunkasa, inda ribar da kamfanoni da masana’antu da ke iya samun ribar da ta zarce dala miliyan 2.7 a duk shekara, ta karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara.
Daga cikinsu, masana’antar ba da hidima ta fi samun bunkasuwa, inda alkaluman ci gabanta suka karu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadinsu shi ma ya karu da kashi 0.4% bisa na bara. Dadin dadawa, saurin sayar da kayayyaki a kasuwa ya karu matuka, ta yadda bangaren samar da kayayyaki da zuba jari ga sana’o’in kirkire-kirkire da sabbin fasahohi suka fi samun saurin bunkasuwa. Kazalika, shige da ficen kayayyaki na samun bunkasa ba tare da tangarda ba, kuma yanayin samar da guraben ayyukan yi na samun habaka yadda ya kamata, yayin da kuma farashin kayayyaki ke raguwa idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
A takaice dai, a wadannan watanni biyu da suka gabata, tattalin arzikin al’ummar Sinawa na bunkasa yadda ya kamata da samun ci gaba a kai a kai, duba da cewa ana ta aiwatar da kyawawan manufofi daga manyan fannoni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp