Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) su rubanya himmarsu domin gudanar da tsare-tsare da za su farfado da tattalin arzikin kasa da kuma samar da saukin rayuwa ga al’umma cikin gaggawa.
A ranar Litinin ne shugaba Tinubu ya ba da wannan umarni ga ministocin yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ministoci biyar da suka hada da na yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris; Ministan Kudi da Gudanarwa na Tattalin Arziki, Mista Wale Edun; Ministan lafiya da walwalar jama’a, Ali Pate; Ministan Noma, Abubakar Kyari; da na Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Anite; da kuma mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale, su ne suka halarci taron.
Da yake bayani jim kadan bayan kammala taron, Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki na Kasa, Edun ya ce, ya gabatar da “Taswirar Tattalin Arziki”, inda ya ce, Majalisar ta amince da cewa lallai tattalin arzikin kasa yana bukatar garan-bawul.
Ya kuma ce Majalisar FEC ta yi nazari kan wasu muhimman abubuwa guda takwas da za a fi maida hankali sosai akansu, tare da ayyana wasu abubuwan da za a aiwatar da su cikin shekaru uku masu zuwa, inda ya kara da cewa, Shugaban kasa ya bukaci ministocin da su fitar da tsare-tsare don habbaka tattalin arzikin kasar.