Kamar kowane mako shafin TASKIRA yakan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi halayyar wasu matan, musamman kan laluben aljihu. Akwai mata da dama wadanda suke da wannan dabi’a ta lalube aljihun mazajensu, wanda mazajen su kan rasa gane dalili ko musabbabin da ya sa matan suke aikata hakan.
Wannan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu. Ko me ya sa wasu matan suke lalube aljihun mazajensu? Me hakan zai iya haifarwa ga mace?
- Halin Da Mata Ke Shiga Sakamakon Rashin Samun Gamsuwa Daga Mazajensu
- Yadda Bukukuwan Sallah Suka Kasance A Garuruwanmu – Mabiya Taskira
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Fatima Tanimu Ingawa, Daga Jihar Katsina:
A tawa fahimtar babban dalilin dake sa wasu matan wannan mummunar dabi’ar ta laluben aljihun mazajensu shi ne rashin tarbiyya, domin duk sauran guragun dalilai da sukan fake da shi na cewar yana da shi bai wadata su duk bai isa hujja ba. Macen da ta koshi da Tarbiyya bata sata, domin wannan ma sa ta ce ka dauki abun da ba naka ba. Babban illar da hakan ka iya jawowa shi ne lalata tarbiyyar yara masu tasowa, tunda in kana son sanin wace ce diya to, dubi uwarta. Haka za ta ginu da wannan muguwar dabi’a zuwa gidan wani ita ma. In ba a yi sa’a ba daga nan za ta koyi ‘yan kananun sace-sace don za ta ga ba komai bane. Bahaushe na cewa inda akuyar gaba ta sha ruwa – nan ta baya ke sha. Haka kuma barewa ba ta gudu – danta ya yi rarrafe. Daga nan an samu tabarbarewar gidaje wanda ke kaiwa ga tabarbarewar al’umma. Shawarata a nan shi ne; mata masu wannan dabi’a ya kamata su gane su daina, su san cewar wannan hanyar ba mai bullewa bace. Ita uwa tushen tarbiyya ce, an santa da gyarawa akoyaushe ba batawa ba. Su dage da ‘yan kananen sana’oin da zai kara rufa masu asiri a kara samun abun masarufi, ta yadda za su kau da kai da abun da bai zama mallakinsu ba. Allah ya sa su gane su gyara.
Sunana Abba Abubakar Yakubu (Marubuci/Dan Jarida), Daga Jihar Jos:
SON ZUCIYA NE DA RASHIN TARBIYYA.
Gaskiya babban abin takaici ne kwarai da gaske a ce mutum ya auri mace barauniya ko mai lalube masa aljihu. Babban abin da ke daga hankalin wasu mazan ma shi ne, idan wannan halayya ta cigaba to, tana iya koyawa yaran da za ta haifa ko su gaji halayyar sata daga jinin da take dauke da shi. Wannan shi ya sa addinin Musulunci ya sanya ka’idar yin bincike kafin aure. Ba kawai bincike na sanin halayyar wanda za a aura ba, har ma da danginta da ‘yan’uwanta ko nasa, domin kaucewa daukar kara da kiyashi. Wani hadisi da aka rawaito daga sahabban manzon Allah (SAWA) na cewa; watarana Annabi Muhammad (SAWA) ya ja hankalin sahabbansa da su kiyaye ciyar da dabbobinsu daga ciyawar kan juji, sai suka tambaye shi mene ne ciyawar kan juji, sai ma’aikin Allah (SAWA) ya ce musu, kyakkyawar matar da ta fito daga mummunan gida. A nan idan mun lura hadisin yana koya mana, mu guji aure daga gidan da babu tarbiyya, domin yana gadarwa zuriya halaye marasa kyau. Komai kyan matar ko dukiyar gidansu. Babu wata mace da za ta fito daga gidan tarbiyya da za ka samu tana nuna halayyar bera a gidan mijinta. Kodayake wasu na cewa; wai idan miji ba ya wadata gidansa alhalin yana da hali, matar tana iya daukar daidai abin da za ta ci. Amma wannan bai hada da laluben aljihun miji ba, wanda karara son zuciya ne da rashin tarbiyya. Na san aure da dama da ya mutu saboda irin wannan halayya, amma a wajena (Allah Ya kiyaye) idan har na lura da wannan halayyar a gidana zan fara ne da nasiha, idan ba ta canza ba zan kai kara wajen waliyyanta, sai in ta kasa dainawa ne zan dauki matakin rabuwa da ita, gudun kar ta bata min tarbiyyar yarana.
Sunana Aisha Isah Abubakar (Aishatu Gama Maiwaka), Daga Jihar Kano:
Da farko dai zan ce rashin tsoron Allah ne, sannan kuma wata kila an saba tun daga gida, wasu kuma gaskiya lefin mazan ne sunada kudin da za su bayar ayi bukatar gida amma ba za su bayar ba kuma ga kudin sunada shi, wanda idan ka bayar aka ci a gida lada ne mara iyaka, sannan idan mace tana satar kudin miji ta sani ba iya ita kadai zai tsaya ba har ‘ya’yanta zai iya shafa, ko ‘yarta mace ta gani ita ma ta je nata gidan mijin ta dora daga inda ta tsaya Allah ya kiyaye. Shawarar da zan bawa mace me irin wannan halin shi ne na farko; ta ji tsoron Allah ta tuna cewar bautar Allah ta zo ba tara abin duniya ba, domin san duniya ne ke shagaltar da mata mu manta da za mu bar wannan duniyar bakidaya sabida haka nake bata shawara tun wuri ta tuba ta daina ta kama sana’a komai kankantar ta za ta taimaka mata wajan dauke kanta da abin hannun mijinta ko ya bata ko bai bata ba, sannan shi ma mijin ya ji tsoron Allah dan kyautatawa yana da dadi kuma yana kara dankon soyayya, amma fa na dawo baya sai kin yi biyayya, kai kuma oga a ji tsoron Allah idan ka kyauta ta wa iyalinka wallahi kai ma Allah zai kyauta ta maka in sha Allah, idan ka bawa matarka kyautar 1k in sha Allah idan ka fita za ka ga Allah ya ninka maka sau ba adadi dan Allah oga. Wadanda ba sa kyauta wa matansu a gwada a bawa uwargida jari, idan ba ita kadai bace a bawa sauran duka, kuma ba wai in ka bayar idan d’and’anon miya ta kama siyarwa idan ka zo sallama ta safe za a fita kada a rage kuzin da aka saba bayarwa, hakan ba zai sa hankalinta ya kai kan aljihun oga ba in sha Allah, Allah ya sa mu dace.
Sunana Mustapha Abdullah Abubakar (Autan Marubutan Jos) Daga Jos Jihar Filato:
Dalilin da ya sa wasu matan suke laluben aijihun mazajensu shi ne; rashin samun kyautatawa daga wajan abokan zamansu, misali; yau a matsayinka na magidance ba sai an ce maka matarka tana bukatar kudin kashewa ba, kafin ka ba ta irin wannan ne ya ke kai wasu mata ga laluben aljihun mazajensu, domin samun kudi don biyan bukatun kansu duk da hakan sun san cewa babu kyau. A gaskiya hakan zai iya haifar da rashin samun fahimta tsakanin ma’aurata bugu da kari zai iya haifar da zargi wanda zai iya zama sanadiyar rabuwan aure ko akasin hakan, mutukar ba su daina laluben aijihun mazajensu ba. Shawara ta ga mata masu irin wannan dabi,a shi ne; su ji tsoron Allah su sani cewa manzon Allah (S.a.w) ranar tashin alkiyama ba zai yi ‘Alfahari da su ba, domin ba su yi koyi da sunnar sa ba na zaman sure, su ma mazaje su sani cewa kyautatawa yanada kyau a zamantakewar aure idan a ce duk sati kana ware wasu kudade kana bawa matar ka ba za ta yi kokarin laluben aijihunka ba.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Naija:
To, laluben aljihun mazaje ga mata ya danganta ya kan zama abu biyu; na daya wata ba tada hali me kyau, kila daman barauniya ce za ta yi masa lalube idan ta ga kucinshi ta kwashe. Abu na biyu kuma; ba mamaki baya kyautata mata a cikin gidan baya bata abin da take so to, ita kuma da zarar ya ajjiye dole za ta lalube ta dauka. Hakan yana nuni da rashin tarbiyya ga mace, wata za ta iya yiwuwa rashin tarbiyyar daga wajen mijin take sabida baya iya bata abin da zao wadatar da ita, wata kuma rashin tarbiyyar tun daga gida take da man can ta saba dauke-dauke. Yana iya haifarwa mace matsala a gaba sabida miji zai iya kasa hakuri da ita ya sake ta, ko ta haifi ‘ya’ya Allah ya jarabce su da irin halin da take. Shawarar da zan bawa mata masu yi shi ne; duk halin da suke ciki su dogara ga Allah, domin Allah yana tare da su, kuma yana tare da duk wani bawa da yake tare da shi, ya san yadda zai yi ya kawo masa mafita. Ga maza kuma idan har kyautatawa matan nasu ne ba sa yi su rika taimaka wa matansu suna wadatasu, idan kuma rashin tarbiyya ne au nuna musu gaskiya domin su gyara kuma su rika taya su da addu’a.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya a lokuta da dama idan ka ga irin wannan matsala tana faruwa idan aka bincika za ka ga laifin mazajen ne ke jawo haka, domin indai namiji yana kyautawa iyalansa zai yi wuya ake samun irin wannan matsala, amma a wasu lokutan akwai matsalar rashin tarbiyya a wajen matan. To magana ta gaskiya hakan zai iya janyowa suke samun yawan sabani da mijin ta, wanda kuma idan hakan yake yawan faruwa zai jawo matsala a zaman aurensu da ka iya kaiwa ga saki. To, shawara a nan ita ce; ya kamata mazaje suke kyautawa iyalansu domin zai taimaka sosai wajen magance irin wannan matsala, su kuma Mata ya kamata su ji tsoron Allah suke hakuri da abun da mazajensu suka ba su, domin komai hakuri ake a wannan al’amarin na rayuwa.
Sunana Aisha D. Sulaiman, Daga Jihar Gombe:
A gaskiya akwai wacce ita daman barauniya ce, kome ka yi mata sai tayi maka sata, akwai wacce kuma yanayi da matsi da takura wanda mijin ya ke saka su ciki ne idan ta rasa yadda za ta yi sai ta daukar masa kudi a aljihu. Shawarata a nan shi ne; idan ya je aiki ya dawo, ya ciro kudin gabadaya ya kirga ya ba ta ya ce ta ajjiye masa da safe zai karba. Na biyu idan haka bai yu ba idan ya zo zai kwanta wannan wandon nasa na ciki gajere ya nemi me aljihu ya zira kudinsa ciki, ai duk tsiya dai ba za a zira hannu a aljihu ana lalube jikinka baka ji ba ko?, wannan a takaice kenan. Abu na gaba kuma idan kankamon namiji ne ya sa take haka, ya kamata kai ka duba ka ga ta ina ka tauye ta, kin ga wata ana daukar kudin cefane dan kadan a bata, har ga Allah a zamanin rayuwar yanzu tun kwanakin ma bare yanzu da muka zo wannan yanayi, Allah dai ya ba mu ikon cinye wannn jarrabawa. Har ga Allah idai har bai isheka ba kuma ba kada tawakkali da hakuri, kuma baki iya ladabi da biyayyar da za ki karba ba, dan ni gani nake sai idan mace ba ta iya karbar ba, indai ki ka iya a lallami da lumana zai dauka ya baki. Shi namiji bai san zafi, zafi baya sa shi yayi miki abu, kowane iri ne, lallami da biyayya da kwantar da kai, yana sakawa yayi bai ma san yayi ba, indai ba masu irin tsattsauran ra’ayin nan ba dan akwai su to, idan me tsattsauran ra’ayi ne ba yadda za ka yi sai ka yi ta addu’a ka fawwalawa Allah abin da ya baka ka yi amfani da shi.
Sunana Sa’idu Mallam Madori Jihar Jigawa:
Hakan dabi’a ce da take haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin ma’auratan, kuma ya kan jawo tabarbarewar tarbiyya ga ‘ya’yan da za su haifa domin su ma sukan iya daukar wannan ta’adar. A takaice ya kan jawo rabuwar aure gabadaya. Shawara ta ga mata masu wannan ta’ada shi ne; su tuba su daina kasancewar ba hanya ce mai bullewa ba, kuma su ma mazajen ya kamata su rika fitar da hakkin matayansu domin zaman lafiya da kuma arziki mai dorewa.
Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia A Jihar Jigawa:
Gaskiya wannan dabi’ar da wasu matan ke yi na laluben aljihun mazajensu ba abu ne mai kyau ba, wanda duk wata macen ƙwarai mai san ta samu alkairin zamantakewar aure da san kuma samun rahamar da za ta iya kai ta ga aljannar da ta ke kafar wannan mijin babu yadda za a yi ta kasance mai yin laluben aljihun mijinta gaskiya. Eh! yin hakan zai iya haifarwa da matan da suke irin wannan halayyar abubuwa kamar haka; wasu abubuwan na rashin jin dadi ga mijin nata kamar :zai rika ganinta da rashin daraja, ƙimarta, zargi zai iya shiga cikin auren nasu, tsana za ta biyo baya, walwalar da ta ke samu ga mijin za ta rago, rashin jituwa kodayaushe zai rika shiga tsakaninsu, da sauran ire-iren wadannan matsalolin da na zayyano. Shawarar farko da ya kamata a bawa matan da suke irin wannan dabi’ar, ita ce su ji tsoron Allah su kuma san cewa hakan da suke yi wa mazajen na su ba zai taba haifar musu da da mai ido ba, dan a karshe idan namiji ya gaji da mace mai irin halayyar nan zai rabu da ita ne ,ya samu wata mai kyakkyawar dabi’a ya aura t9, kun ga wa gari ya waya?. Sai kuma su mazan da suka tsinci kansu ga irin matan nan, da su yi hakuri sannan kuma a duk lokacin da suka fahimci matansu na da irin halayyar nan, su daina yin wasarere da dukiyar su, su zama masu taskance ta, inda suka san matan za su iya gani. Allah ya sa mu dace ya shiryar da mata masu irin wannan dabi’ar.
Sunana Alhassan Bununu Abdulrahman, Daga Jihar Bauchi:
Ni a nawa ganin abun da ya sa mata suke caje aljihun mazajensu abu na farko shi ne; rashin samun cikakken tarbiyya daga wajan iyaye musanman iyayenmu mata da kuma kawayen banza, za ka ga wani lokutan akan abun duniya za su ke bawa ‘ya’yansu ko kawayensu shawara akan suke dan duba aljihun mazajensu domin matukar mazan sunada dan wadata koda kuwa ‘yar ba ta so za su tilasta mata su ce; “in kin zaunawa namiji sai ya ba ki za ki ta zama a haka ko kuma a ce za ki mutu marainiya ki duba wance ga waccen ma”, ita kuma uwa tana ganin ita ta haife ta kuma in ta saba mata za ta yi fushi da ita, kuma ‘yar sai ka ga ta fara a tsorace da zarar an yi nasara to nan kuma abun da ba a so zai faru, shi ne rashin yarda da zarar ya gane. Abun da mata ba su gane ba su suke nemawa iyayensu daraja a gun mazajensu ta hanyar zamantakewa in namiji ya raina iyayenki ke ce, haka ma in ya girmama su ke ce.
Sunana Aisha T. Bello, Daga Jihar Kaduna:
Sata na janyo zubar mutunci sosai, na ga in da miji ya kama mace na sata cikin aljihunsa mutucin ya zube wulakanci da cin mutunci zai biyo baya. Gaskiya yana haifar da matsala sosai dalili kuwa shi ne yana haifar da rashin jituwa ga ma’aura ta, kuma in da yara wanan ma matsala ce, saboda in ita ce za ta yi masu tarbiyya, in tana sata kuma yara za su koya kuma tana iya kaiwa ga rabuwar aure. Shawarata a nan shi ne; ga masu irin wanan hali su ji tsoron Allah su daina saboda ba hali bane laluben aljihun miji ba zai haifar da da mai ido ba Allah ya sa mu dace.