Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi magana ne akan Ƙurajen Fuska.
- CMG Da Kwamitin Wasanni Da Olypimcs Na Faransa Za Su Zurfafa Hadin Gwiwa
- Sirrin Albasa Wajen Inganta Lafiyar Dan Adam
Ƙurajen taya-ni-muni:
Ƙurajen (pimples) a turance ko in ce (Bulgaris) a likitance, suna ɗaya daga cikin larurori masu addabar samari da ’yanmata. Suna fitowa ne a daidai lokacin girma, domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke yawa a jinin samari maza da kuma wasu kadan daga cikin mata. Wannan sinadari shi ke da alhakin sa maiko ya rika taruwa a fuska. Idan maiko ya taru a fuska sai kwayoyin cuta su zo su taru a wurin su kawo kurji.
Hanyoyin kariya su ne:
Kiyaye taruwar maiƙo da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara:
1- Rage maiƙo a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kicin wafif ko tawul ko tushu mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye.
2- Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma.
3- Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai –a-kai ya kan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta.
4- Ga wanda wadannan
Dabaru ba su yi musu aiki ba, za su iya zuwa su nemi man shafawa na fuska da kirji mai dauke da sinadarin benzoyl perodide na shafawa safe da yamma bayan an wanke fuska.
5- Idan hakan ta ki wadatarwa sai an je asibiti an hada da karbar magungunan kashe kwayoyin cuta. 6- Ga wadanda wannan ma bai yi aiki ba, akwai dai magunguna masu karfi, har ila yau irin samfurin bitaman ‘A’ da ake kira isotretoin da ake rubutawa a asibiti. Akan samu nasara sosai idan aka jarraba wadannan. Amma ba a ba wa mai juna biyu shi.
7- Ba a so a rika matse kurajen saboda hakan kan iya jawo tabo, an fi so a bar su su fashe da kansu sai a wanke wurin. Allah ya sa mu dace
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp