Daga ran 24 zuwa ran 27 ga wata, zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, kana jami’i mai kula da harkokin hukumomi da jami’ai na jihar Wang Weiping, ya jagoranci wata tawaga domin ziyartar kasar Niger bisa gayyatar da aka yi musu.
Yayin ziyarar, Wang Weiping ya gana da firaministan kasar Lamine Zeine, inda suka yi musayar ra’ayi kan zurfafa hadin gwiwar kiwo lafiya da sada zumunta tsakanin al’ummomin jihar Guangxi da kasar Niger da sauransu.
- Tawagar Jiragen Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Ta Tafi Masar Domin Halartar Wani Bikin Nune-Nune
- Sin Ta Fara Aiwatar Da Manufar Rangwame Domin Bunkasa Cinikayyar Musayar Kayayyakin Amfani A Gidaje
Yayin ziyarar tawagar, an yi bikin mika na’urorin jiyya da magunguna da Sin ta baiwa kasar Nijar kyauta a asibitin abin koyi na Niamey.
Kazalika, tawagar jami’an lafiya ta Sin dake kasar Nijar da likitocin asibitin al’ummar jihar Guangxi ta kasar Sin da asibitin abin koyi na Niamey, sun yi hadin gwiwar ba da jiyya kyauta, inda suka yi wa mutane 5 tiyatar zuciya, da jinyar mutane fiye da dubu da rarraba magunguna da binciken lafiyarsu. Lamarin da ya samu karbuwa sosai wajen al’ummar wurin.
Baya ga haka, tawagar dake karkashin jagorancin Wang Weiping ta gai da mambobin tawagar jami’an lafiya na Sin dake kasar Nijar. Tun daga shekarar 1976, jihar Guangxi ta tura tawagogin jami’an lafiya har sau 24 wadanda suke kunshe da likitoci 756 zuwa kasar Nijar. (Amina Xu)