A jiya Litinin 15 ga wata ne, aka bude taro karo na 11, na kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar dakile cin hanci da rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya, a birnin Doha na kasar Qatar. Inda Madam Hua Chunying, mataimakiyar ministan harkokin waje ta kasar Sin, wadda take jagorantar tawagar kasar Sin domin halartar taron, ta yi jawabi a bikin kaddamar da taron.
A cewar Madam Hua, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna tsayawa tsayin daka wajen yaki da cin hanci da rashawa. Ta ce, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai tarihin fiye da tsawon shekaru 100 ta dade tana rike da ragamar mulki, inda wata mihimmiyar dabara da jam’iyyar ke dauka ita ce tabbatar da cikakkiyar da’ar mambobinta, da kokarin yaki da cin hanci da rashawa ba tare da kasala ba.
Jami’ar ta kara da cewa, duniyarmu na fuskantar kalubaloli iri-iri. A kokarin tinkarar yanayin da ake ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya, wadda ta nuna hanyar da ya kamata a bi wajen gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban don dakile cin hanci da rashawa. Wato ya kamata a yarda da daidaiton ikon mulkin kai na mabambantan kasashe, da bin dokokin kasa da kasa, da la’akari da ra’ayoyin kasashe daban daban, da dora muhimmaci kan moriyar jama’a, da aiwatar da takamaiman matakai a kokarin tabbatar da amfaninsu. Ban da haka, kamata ya yi a sauke nauyin dake bisa wuya kamar yadda yarjejeniyar dakile cin hanci da rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta kayyade, da dora muhimmanci kan ayyukan cafko masu aikata laifi da suka tsere, da dawo da kudin da suka sata, da kulla tsarin hadin gwiwa mai amfani, da kin ba da kariya ga wadanda suka aikata laifi, a kokarin kafa wani tsarin kula da ayyukan dakile cin hanci da rashawa a duniya mai cike da adalci da kima.
Yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce nau’in yarjejeniya mafi muhimmanci, kuma mafi tasiri a duniya, wadda ta samu kasashe 192 da suka saka hannu a kanta. Kuma baki daya, za a kwashe kwanaki 5, ana gudanar da taro mai nasaba da yarjejeniyar a wannan karo. (Bello Wang)














