Mahukuntan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United sun tabbatar da cewar babban mai horar da ƙungiyar Eric Ten Hag zai ci gaba da kasancewa a matsayinsa a kakar wasa mai zuwa.
Tun da farko anyi ta raɗe raɗin cewar tsohon kocin na Ajax zai bar Old Trafford a ƙarshen kakar wasa ta bana, amma doke Manchester City a wasan ƙarshe na FA Cup ya sauya wa mahukuntan Manchester United ra’ayi akan ɗan ƙasar Holland din.
- Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?
- Yau Za A Kece Raini Tsakanin Arsenal Da Manchester United A Old Trafford
Ten Hag ya lashe kofuna biyu tun bayan zuwan shi Manchester United a shekarar 2022 inda ya maye gurbin Ralf Ragnick, a shekararsa ta farko a Old Trafford ya lashe kofin EFL sai kuma bana da ya doke City a wasan karshe na FA Cup a filin wasa na Wembley Stadium.
Akwai yiwuwar nan gaba kaɗan mahukuntan ƙungiyar su tattauna da Ten Hag akan ƙarin kwantiragin shekaru da ake hasashen zasu iya haura shekaru biyar idan ya amince da sabon tayin da zasu yi mashi.