Shugaban Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFund), Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya ce hukumar gudanarwar hukumar ta amince da fitar da sama da Naira biliyan 100 ga manyan makarantun kasar nan domin bunkasa kokarinsu na horar da dalibai kan ilimin likitanci.
Aminu Bello Masari ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Katsina.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka
A cewarsa, an dauki matakin ne saboda muradin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an magance karancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya da kuma hana wasu guduwa zuwa wasu kasashe.
“Shugaban kasa ya damu musamman da yanayin da kuma yadda lamarin ke shafar tsarin kiwon lafiyar Nijeriya, yana so ya kafa matakan da za su ba da damar farfado da tsarin kiwon lafiya ta hanyar tsare-tsare irin wannan shiga tsakani na TETFUnd.
“Mun zabo manyan makarantu guda uku a kowace shiyyar siyasar kasar nan, inda kowace cibiya ta karbi Naira biliyan 4 don gudanar da ayyuka da fadada ilimi musamman don kara karfin daukar dalibai da horar da dalibai a fannin ilimin likitanci.
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi.
Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan 1.6, wanda ya haura daga kaso 3 na harajin ilimi da aka dora wa ribar kamfanonin da ke kasuwanci a Nijeriya kamar yadda dokar TETFund ta tanada.
Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an fitar da Naira biliyan 225 zuwa asusun bayar da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND), domin shirin rancen daliban gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp