Jami’an kashe gobara a Jihar California dake Yammacin Amurka a mulkin Donald Trump sun maida hankali wurin kashe wutar daji da ta tashi a Arewa maso Yammacin Los Angeles wanda ta riga ta zama daya a cikin wautar daji da suka fi yin barna a tarihin jihar.
Wutar daji da aka mata lakabi da Thomas ta kona fillayen daji da ya kai kilomita 930 kana ta lalata gine gine 800 a Karamar Hukumar Santa Barabara tun lokacin da ta fara a makon da ya gabata.
- An Fitar Da Rahoto Game Da Mummunan Tasirin Salon Matsin Lamba Na Diflomasiyyar Amurka
- Ninkayar Kano A Kogin Basukan Gida Da Daji
Hukumomi sun ce kashi 10 na harshen wutar ce aka kashe, kuma a yayin da masu kashe gobarar ke samun nasara ta sama, wutar na ci gaba da zama mai hadari da za ta iya yaduwa cikin gaggawa ta iska.
Jami’ai 750 ne suke aikin kashe wutar da ake kira Thomas, wacce ta fi ci a Kudnacin California.
Wutar ta tilasta kwashe mutane 200,000 daga gidajensu. Adadin mutane ya karu ne a ranar Lahadi yayin da aka kwashe mutane masu yawa a Santa Barbara, a lokacin da wannan gagarumar wuta take kara bazuwa a yankin.
Shugaba Donald Trump ya dau mataki a ranar Juma’a a kan wutar, inda ya ayyana dokar ta baci ta tarayya a Califonia, wanda ya bai wa hukumomin tarayya daman shirya kai dauki.
Yadda masifar wutar ta yi barna a yankunan Jihar California
Babbar wutar dajin nan dake cin yankuna masu yawa a kewayen birnin Los Angeles na Jihar California a nan Amurka, yanzu haka an ayyana ta uku a girma a tarihin jihar, da barnar da ta yi wadda tazo dai-dai da gobarar shekarar 2013 ta hanyar kona sama da hekta 800.
Jami’an agajin gaggawa sun ce wasu ‘yan kwana-kwana 8,000 daga sauran jihohi suna California don taimakawa a kashe gobarar dajin, ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu da manyan motocin kashe gobara.
An kiyasta kudaden da aka kashe akan aikin kashe gobarar kusan Dala Miliyan 89.
A jiya Asabar ne jami’an ‘yan kwana-kwana suka ce gobarar dajin da aka yi wa lababi da Thomas fire, wadda ta fara tun farkon watan Disamba, yanzu haka ta kona kusan hecta dubu 105. An shawo kan kashi 40 cikin 100 na wutar, amma jami’ai sunce gine-gine kimanin 18,000 na fuskantar barazana, kuma iska mai karfi na iya haddasa wata gobarar.