Wanann wani takaitaccen nazari ne da wakilinmu na Adamawa Muh’d Shafi’u Saleh yayi, game da tsayar da Sanata Aishatu Dahiru Binani takarar kujerar gwamna da jam’iyyar APC tayi, bayan ta kada ‘yan takara 5, da suka tsaya takarar fidda gwanin kujerar gwamna karkashin jam’iyyar a shirinta na shiga babban zaben 2023, kada mutum biyar ta tayi a zaben ya bude sabon shafi a siyasar jihar da sake fito da tasirin da mata ke yi a harkokin siyasa da dimokradiyya a Nijeriya.
Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, da’aka haifa a 11 ga watan takwas na shekarar 1971, ta kasance mace ta farko da’aka zaba a matsayar ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Yola ta kudu, Yola ta arewa da Girei, a shekarar 2011-2015, a shekarar 2019 ne kuma aka zabeta a matsayar sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya da ya hada kananan hukumomi bakwai, a majalisar dattawa ta kasa.
Zaben Sanata Binani, a matsayar sanata ya bayyanar da wasu muhimman abubuwa tattare da ita da siyasar jihar da zaben, domin kuwa zaben shine na farko da’aka shaidi yawan kuri’u a lokacin zaben, ta lashe zaben da yawan kuri’un da ba’a taba ganin wani dan siyasa ya lashe kujerar da yawan kuri’u kamar wanda ta lashe zaben dashi a zaben 2019 ba.
Binani, ta taka muhimmiyar rawa, wajan kyautatawa da inganta rayuwar jama’ar da take wakilta, wanda hakan ya sa ta samu karbuwa da haskawa a idanun jama’a da siyasar jihar Adamawa, domin kuwa kyautatawarta, ba kawai ya tsaya ga jama’ar mazabarta ko kananan hukumomin da take wakilta bane a’a, ta fadada ayyukan da takeyi ga sauran sassan kananan hukumomin jihar Adamawa.
Wannan tsari da manufar siyasar Binani, ya bata damar samun darewa kujerar ‘yar majalisar dattawa cikin ruwan sanyi, da dinbin kuri’un da ba’ataba ganin wani da ya hau kujerar da yawan irin wadannan kuri’un ba.
Binani, tana darewa kan kujerar ‘yar majalisar dattawa batayi kasa a gwiwa ba, wajan fadada manufar siyasarta ba, domin kuwa rike kananan hukumomi 9 cikin 21, yasa ta maishe da kanta tamkar jihar Adamawa take wakilta, don kuwa tana a matsayar ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, amma jinkai da kyautatawarta ga jama’a ya karade yankuna da sassan kananan hukumomin jihar baki daya.
Wasu daga ayyukan da ta yi, sun hada da samar da wutar Sula ga jama’a ba tare da nuna sonkai ko wariya ko la’akari da addini ko guri ba, da kusan kowani lungu da sakon kananan hukumomin jihar ta kai da kafa wutar lantarkin sula, samar da fanfon ruwansha da fanfonan tuka-tuka, shirin inganta kiwon lafiya da magunguna, taimakawa manoma, bunkasa harkokin sana’o’in dogaro da kai ga matasa maza da mata, da taimakon kai-tsaye, suna daga dalilan da yasa Binani ta samu karbuwa, musamman kuma a idanun matasa mata da maza.
Duk da Binani, ta dade da mafarkin zama gwamnan jihar Adamawa, amma bata himmatu da kokarin tabbatar da cikar burinta ba, sai lokacin da jam’iyyarta ta APC ta mata barazar ba zata bata tikitin tsayawa takara ba, domin kuwa ta tabbata Abdul’aziz Nyako, da ta kwace kujerar a hannunsa, jam’iyyar zata dawo dashi, shi zata baiwa tikitin takara a zaben 2023.
Binani batayi kasa a gwiwa ba, ta nuna sha’awarta ta tsayawa takaran kujerar gwamna, duk da ta gamu da tirjiya daga wasu magoya bayanta da daidaikun dattawa ko manyan jihar, a lokaci guda kuma, ta samu karfafawa daga dinbin magoya baya, musamman ganin gazawar da mazan sukayi, wajan shawokan matsalolin da kullum ke karuwa ga jama’a.
Hakan ya kara mata karfin gwiwa, inda ta zafafa kokarin cimma burinta, ta ci gaba da shirye-shiryen ganin burinta ya cika, wannan yasa ta koduri aniyar ko bata samu tikitin takara a APC ba, zata koma wata jam’iyya, da nufin tsayawa takarar kujerar gwamna a babban zaben 2023, duk da kokarin nusarwar da wasu ke mata ciki kuwa harda Malamai.
Malamai da dattawa da dama, sun nuna rashin gamsuwa da Binani ne a matsayin na mace, saboda ganin da suke mata cewa ita mace ce, shugabancinta zai iya zuwa da raunin gaske, wanda hakan ka iya kawowa jihar da alummarta koma baya ta fuskoki da dama, to sai dai wadannan dalilai basu taba kashewa Binani gwiwa na sai ta kafa tarihin zama mace gwamna ta farko a jihar dama Nijeriya ba.
Kan haka, Binani ta shiga jerin ‘yan takaran kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC, bayan da aka gudanar da zaben fidda gwanin sai gashi ta fito da gagarumin rinjayen kuri’u 430, cikin 1075, lamarin da ya zo wa mutane da dama da mamakin gaske, domin na biyu ko uku da dama aka dauka zatazo a zaben, duk da gaf za’a fara zaben bakin Zare ya nuna.
Binani, da koduri aniyar ko ta fadi zaben fidda gwanin, ba zata hakora ba, ta shirin tsaf da nufin ficewa daga jam’iyyar ta koma wata, domin tabbatar da cikar burinta, na ganin ta kafa tarihi da hakakkar burinta na zama gwamnan jihar Adamawa.
To sai dai samun tikitin tsayawa takarar da Binani tayi, ya bude sabon shafi a siyasar jihar, ta yadda mata ke ganin suma yanzu dama ta zo musu, don haka nasarar nata ya sake dinke harkokin jama’a da siyasar jihar musamman mata, suna ganin ta fado musu gasassa, yanzu haka mata ba tare da la’akari da kabila, inda ka fito ko addini ba, sun goyi bayan na su, da tunanin zasu kafa gwamnati, su ne kwamishinoni, sakataren gwamnati da sauran mukamai, wato dai yadda sukaso haka gwamnatin za’a tafiyar da ita.
Babu tababa tsayawa takarar Binani a zaben 2023, ya bude sabon shafi a harkokin siyasar ba kawai a jihar Adamawa ba, Binani tana da tasirin da zata iya lashe zabe, wanda kada manyan ‘yan takaran da kowannensu ke ji da kansa, babbar alamace na cewa lashe zaben kujerar gwamna ba zaizo mata da wahala ba.
Da take amsa tambayoyin ‘yan jaridu a Yola, Aishatu Binani ace “Na shirya na fuskanci gwamnati maici, kuma jam’iyya na zata fito da tsare-tsaren da muke da karfin gwiwar lashe zabe, lokacin da muka fito da tsare-tsarenmu, PDP zata fahimci ba ta da madogara a zaben 2023.
“Nasaran da na samu nasarace na mu baki daya ‘yan takara, muna da yarjeneniya tsakaninmu kafin mu shiga fagen zabe, na goyon bayan duk wanda yayi nasara a tsakaninmu, na yaba ga kowani a cikinmu da halin girmamawan da suka nuna mini, da cewa za su sauke nauyin da yake kansu.
Ta kuma ce “na samu nasarar lashe zaben fidda gwanin ne da goyon baya da hadin kan da matan suka bata, shigo da mata masu zabe biyu-biyu daga kowace unguwa, ya samar da mata masu zabe 452 a cikin masu zabe 1130, da suka yi zaben, wannan itace gagarumar damar da ta kaini ga yin nasara a zaben, nasara na, zan yi aiki ne da kudurorin duka mata, ba kawai a Adamawa ba harma a kasa baki daya, da nasara na, fatan da yaya mata ke dashi zai tabbatu, wata rana za su cimma burin da suke dashi” inji Binani.
To sai dai akwai kalubale da daman gaske da yake tattare da cikar wannan burin na ta, domin kuwa baya ga matsalar da zata fuskanta daga malamai da kungiyoyi na addinin Musukunci, da suke ganin akwai nakasu a shugabancin mace, su kansu ‘yan takaran da suka tsaya takara tare da yi nasara a kansu, ba kyaleta sukayi ba, domin kuwa Malam Nuhu Ribadu, da ya zo na biyu a zaben bai daddara ba, ya rubuta koken kan cewa anyi amfani da kudade an saye kuri’u lokacin gudanar da zaben.