ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista

by Sadiq
5 months ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu bai taɓa ba shi umarnin yin ƙarya, ya tsare, ko ya gallaza wa kowane ɗan jarida ba, ko da kuwa suna suka gwamnatinsa.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a Abuja.

  • UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
  • Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu

Ministan ya bayyana cewa, ko da wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai ko furucin wasu mutane na zama masu zafi ko ɓatanci, Shugaba Tinubu bai taɓa ce masa ya ɗauki matakin ramawa ba.

ADVERTISEMENT

“Wasu lokutan kafafen labarai kan tayar da hankali,” in ji shi.

“Amma Shugaba Tinubu bai taɓa cewa na yi ƙarya ko na sauya gaskiya ko na kama masu laifi ba.”

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka.

Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.

Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana.

“Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi.

“Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.”

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba.

Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya.

Ya kuma bayyana wani babban ci gaba da aka samu a Nijeriya na dab da samuwa domin za a karɓi baƙuncin Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Hanyoyin Yaɗa Labarai (MIL) a Jami’ar Open University da haɗin gwiwar UNESCO.

Wannan cibiyar za ta taimaka wajen ilimantar da mutane kan labaran ƙarya da yaɗa jita-jita.

“Da zarar an amince, mutane daga sassa daban-daban na duniya za su riƙa zuwa Nijeriya domin koyon dabarun kafafen yaɗa labarai,” in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda

Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu 'Yan Ta’adda

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.