Shugaba Bola Tinubu, ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), inda suka yi wata ganawar sirri a gidansa da ke Jihar Neja.
Tinubu ya zarce gidan tsohon shugaban kasar bayan halartar taron kaddamar da shirin manoma da Gwamna Mohammed Umaru Bago ya aiwatar a Minna, babban birnin Jihar Neja.
- SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1
- Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer
Tinubu ya ziyarci Jihar Neja a ranar Litinin domin ziyarar aiki ta kwana daya domin kaddamar da gyaran tashar jirgin saman Minna wanda yanzu aka sauya masa suna zuwa Bola Ahmed Tinubu, da sauran wasu ayyuka.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, Shugaba Tinubu ya kai ziyara tare da shafe sama da sa’o’i guda yana tattaunawa da Janar Babagida, wanda shi ne shugaban mulkin sojan Nijeriya daga 1985 zuwa 1993, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kan iyakokin kasar nan.
An tattaro cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umarci Bago ne, kadai ya halarci ganawar sirrin da aka yi tsakanin shugabannin biyu.
An ruwaito cewa ya bai wa Tinubu shawara kan shirye-shiryen da gwamnati za ta yi na inganta rayuwar talaka, ya kuma yi alkawarin bai wa Tinubu shawara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.