Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana alhininsu game da rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu yana da shekaru 68.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa , Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Dokta Abdulaziz a matsayin ginshiƙi wajen koyar da tarbiyya da kyawawan ɗabi’u.
- Tinubu Zai Yi Amfani Da Dokar Ta-ɓaci Wajen Tsoratar Da Gwamnoni Gabanin Zaben 2027 – Amaechi
- APC Ta Musanta Zargin Sauya Kashim Shettima A Zaɓen 2027
“Dokta Abdulaziz ya kasance murya mai ƙarfi wajen kira zuwa gaskiya da ɗabi’u masu kyau.
“Ya tsaya tsayin daka wajen yaƙar tsattsauran ra’ayi, musamman a farkon fitowar Boko Haram, inda ya yi amfani da iliminsa da tasirinsa wajen wayar da kai da kawo zaman lafiya,” in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban ya ƙara da cewa al’ummar Musulmi za su yi matuƙar kewar Dokta Abdulaziz saboda faɗakarwarsa da kira zuwa adalci da gaskiya.
Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa.
Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin.
Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta.
“Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da almajiran Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
“Dokts Dutsen Tanshi ya kasance abin tunawa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci.
“Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Kwankwaso.
Dokta Abdulaziz ya kasance mashahurin malami wanda aka san shi wajen faɗar gaskiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma, musamman a Arewacin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp