Shugaba Bola Tinubu ya amince da kudirin kafa jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya bayyana hakan ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa don kafa cibiyar kula da lafiya ta tarayya a garin Kafanchan, jihar Kaduna.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ta bayyana cewa, Shettima ya bayyana hakan ne a karshen mako a wata ziyarar ta’aziyya ga iyalan Fasto Kukah kan rasuwar mai martaba Yohanna Sidi Kukah, Agwom Akulu na masarautar Ikulu kuma dan gidan Bishop Matthew Hassan Kukah na cocin Katolika ta Sokoto.
“Tare da Sanata Katung da dan majalisar wakilai, mun tuntubi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kuma ya amince a kafa jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna,” in ji Shettima a ziyarar da ya kai Masarautar Ikulu, Kamuru a karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp