Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya baro birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil bayan halartar taron BRICS na shekarar 2025.
Jirgin shugaban ƙasa mai lamba 001 ya tashi daga sansanin sojin saman Galeao da ke Rio de Janeiro da misalin ƙarfe 12:50 na rana agogon Brazil.
- Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya
- An Sanya Kaburburan Sarakunan Daular Xixia Ta Kasar Sin Cikin Muhimman Wuraren Tarihi Na UNESCO
Shugaba Tinubu ya samu gayyata daga shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, domin halartar taron.
Ya yi jawabi a ranar farko ta taron na shugabannin ƙasashe masu tasowa.
A jawabin da ya gabatar, Tinubu ya ce akwai buƙatar a sake duba yadda ake tafiyar da tsarin shugabanci na duniya, tsarin kuɗi da na lafiya, domin a tabbatar da adalci da haɗin kai ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da masu tasowa, musamman a Afirka.
Ya jaddada buƙatar samar da tsarin adalci da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar cin moriyar ci gaban fasaha da samun rance cikin sauƙi daga ƙasashen duniya.
Ya kuma bayyana yadda Afirka ke fuskantar manyan matsalolin muhalli duk da cewa ba ta fitar da gurbataccen hayaƙi sosai.
A gefe guda kuma, Tinubu ya bayyana shirye-shiryen gyaran da gwamnatinsa ke yi, ciki har da amfani da makamashi, yaƙi da sauyin yanayi, gina birane da kuma inganta harkar kiwon lafiya ga kowa.
Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran ƙasashe masu tasowa.
Jawabin Tinubu a taron BRICS na 2025 ya nuna matakin farko da Nijeriya ta taka a matsayin ƙasa mai ƙawance da BRICS.
Nijeriya ta zama ƙasa ta tara da aka ƙara a cikin BRICS a watan Janairu 2025, tare da ƙasashen Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekistan.
Kafin ya isa Brazil, Shugaba Tinubu ya tashi daga Nijeriya a ranar 28 ga watan Yuni zuwa Saint Lucia, inda ya ƙulla dangantakar diflomasiyya da ƙasar da kuma ƙungiyar ƙasashen gabashin Caribbean wato OECS.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp