• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Bukaci Manyan Masu Kalubalantarsa Atiku Da Obi Da Su Janye Daga Takara

Ya Samu Sarautar Gargajiya A Delta

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Tinubu

Dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shawarci manyan abokan karawarsa, Atiku Abubakar da Peter Obi da su hakura su bar masa neman shugabancin kasar nan.

Tinubu, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a  masarautar garin Gbaramatu da ke karamar hukumar Warri a kudu Maso Yamma, ya ce, Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya jima lokuta da dama yana neman kujerar ba tare da ya samu nasara ba, don haka da bukatar ya janye muradinsa na sake neman a 2023.

  • Zamanintar Da Sha’anin Gona Da Kauyuka Ya Dogaro Da Halin Da Ake Ciki Da Muradun Jama’a
  • Ko Kun San Gida Mafi Tsada A Duniya?

Da ya ke magana da Pere na Gbaramatu, Oboro-Gbaraun II, Aketekpe, Agadagba da kuma dandazon magoya bayansa a masarautar Basaraken, Tinubu ya ce: “Sau nawa Atiku na neman mulkin nan? Ko da yake Atiku na kan nema, ku fada masa ya koma gefe kawai ya zauna, hakan ya isa.”

Kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, Asiwaju Bola ya ce, lissafin kididdigar Obi da nazarinsa kan tattakin arziki dukkaninsu cike suke da tukin kuskure.

“Ba na son jero sunaye, yana tunanin kididdigar da zai bai wa ‘yan Nijeriya abinci ne? Ya na bada kididdiga marar kyau, tattakin arziki marar kyau. Ba wannan al’ummar Nijeriya ke bukata ba,” Tinubu ya fada wa Obi.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Tinubu, wanda aka nada masa Sarautar Iyelawei na masarautar Gbaramatu Kingdom da Sarkin ya ba shi, ya sha alwashin cika dukkanin alkawuran da ya yi, ya kuma yi alkawarin samar da abubuwan cigaba ga al’ummar Gbaramatu, musamman a bangaren shimfida titina, Jami’a, da sauransu, ya ce ba zai taba yin nisa da masarautar ba.

“Zan ci gaba da neman shawarorin Sarki domin cigaban masarautar Gbaramatu, don yin aiki wajen bunkasa tattalin arziki”.

Wadanda suka yi wa Tinubu rakiya sun hada da gwamnonin Kano, Abdulahi Ganduje, Mai Mala Buni na Yobe; karamin ministan albarkatun Mai, Timipre Silva; karamin ministan kwadago, Festus Keyamo; Dimeji Bankole, da tsohon ministan kula da harkokin Niger Delta Affairs, Elder Godsday Orubebe, da sauransu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
Manyan Labarai

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Next Post
Gwamnatin Kaduna Ta Jajanta Wa Iyalan Mutane 15 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

Gwamnatin Kaduna Ta Jajanta Wa Iyalan Mutane 15 Da 'Yan Bindiga Suka Kashe

LABARAI MASU NASABA

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.