Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya roƙi ƴan ƙasar su riƙa yi wa shugabanninsu addu’a, inda ya bayyana cewa ƙasar na kan hanyar dawowa kan turba.
A cikin sanarwar da ya fitar don taya mabiya addinin Kirista murnar Kirsimeti, Shugaba Tinubu ya ce yana buƙatar ‘yan Nijeriya su ci gaba da yi wa ƙasa da shugabanninsu addu’a a kowane mataki.
“A wannan ranar Kirsimeti mai cike da farin ciki, ina taya Kiristoci murnar wannan rana a Nijeriya da duniya baki ɗaya,” in ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa Kirsimeti tana nuni da haɗin kai, ƙaunar juna, da zaman lafiya.
Shugaba Tinubu ya kuma yi jaje ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a turmutsitsin rabon abinci a Abuja, Ibadan, da Anambra, inda ya yi addu’ar Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba.