Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi, rasuwa a safiyar yau Laraba 25 ga watan Disamba 2024.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan Hamisu Muhammad Gumel, ne ya shaida haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
- Tinubu Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Riƙa Yi Wa Shugabanni Addu’a
- Gwamnatin Tarayya Ta Wanke Mutane 888 Daga Zargin Ta’addanci
Sanarwar ta tabbatar da za a yi jana’izarta da karfe 4:30 na yamma a garin Kafin Hausa da ke jihar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya roki Allah Ya sa mutuwa ta zama hutu a gare ta tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalanta.