Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Brasilia, babban birnin ƙasar Brazil, domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kan gayyatar takwaransa, Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva.
Wannan ziyara na nuni da sabon yunƙurin ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi da siyasa tsakanin Nijeriya da ƙasar Brazil, wacce ita ce mafi girma a Latin Amurka. Ana sa ran wannan tafiya za ta haifar da jarin biliyoyin daloli musamman a ɓangaren noma, da makamashi, da fasahar zamani.
- Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa
- Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
A lokacin ziyarar, Shugaba Tinubu zai gudanar da tattaunawa ta musamman da Lula da Silva, sannan kuma zai halarci Taron Kasuwanci tsakanin Nijeriya da Brazil, inda zai gana da manyan masu zuba jari. Haka kuma, za a sanya hannu kan muhimman yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna (MoUs).
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, babban abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne aiwatar da jari a fannin noma da aka daɗe ana tattaunawa a kai, ciki har da ci gaba da aikin $1.1 biliyan Green Imperative mechanisation project, da kuma jawo sabbin jarin ƙasashen waje a ɓangaren noma da makamashi.
Haka kuma, jami’an gwamnati sun bayyana cewa wannan ziyara za ta ƙara haɗin gwuiwa a fannin sufurin jiragen sama, da sabunta makamashin, da musayar al’adu, da sauyin fasahar dijital.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp