A yau Laraba ne zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya isa Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu domin jama’ar jihar su bai yi zababben shugaban kasar tarba mai kyau.
- Buhari Zai Halarci Nadin Sarautar Sarki Charles A Landan
- Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni
Wike da mukarrabansa sun tarbi Tinubu a filin jirgin sama na Fatakwal lokacin da jirginsa ya sauka da misalin karfe 10:03 na safe.
Magoya bayan gwamnan kuma sun halarci tarbar Tinubu.
Za kuma a shirya wa zababben shugaban kasar liyafar cin abinci da yammacin ranar Laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp