Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa birnin Dar es Salaam, Tanzania, domin halartar taron makon Makamashi na Afrika, wanda zai fara a ranar Litinin, 27 ga Janairu. Ya samu tarɓa a filin jirgin sama daga Ministan harkokin waje na Tanzania, Amb. Mahmoud Thabit Kombo, na hukumar jakadancin Nijeriya a Tanzania, Amb. Salisu Suleiman.
Taron na kwana biyu zai gudana tare da goyon bayan gwamnatin Tanzania, tarayyar Afrika (AU), da bankin ci gaban Afrika, da bankin Duniya.
- Faduwar Darajar Naira Ya Haifar Da Raguwar Kayan Da Ake Shigowa Da Su Nijeriya
- Nijeriya Ta Gurfanar Da Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci Da Kuɗaɗe Fiye Da 100 A Cikin Shekaru 2 – Tinubu
A ranar farko, ministoci daga ƙasashe daban-daban, ciki har da Nijeriya, za su gabatar da manufofin makamashin ƙasashensu, wanda ake kira “compacts”, suna bayyana hanyoyin da za su bi wajen samun damar makamashi ga kowa a cikin shekaru biyar. A ranar ta biyu, Shugabannin ƙasashen za su amince da sanarwar Makamashi ta Dar es Salaam, wanda zai samar da tsarin ci gaban bai ɗaya don cimma manufofin Ƙudirin 300 na Afrika.
Shugaba Tinubu zai gabatar da sanarwa ta ƙasa wanda zai sake tabbatar da kudirin Nijeriya na samun damar makamashi ga kowa da jagorancin ta a fannin makamashi na Afrika. Hakanan zai bayyana ci gaban Nijeriya a makamashi mai tsabta da dabarun ta na samar da ingantaccen makamashi a nahiyar.
Ministan Harkokin Waje na tarayyar Nijeriya, Amb. Bianca Odumegwu-Ojukwu; da Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, da Mai ba da Shawara na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Makamashi, Olu Verheijen, da sauran manyan jami’an gwamnati na daga cikin ƴan rakiya.