Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da babban sabon aikin noma na zamani da zummar kara samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Har ila yau, shirin ya kunshi rabar da kayan aikin noma na zamani daidai har guda 9,022, wadanda suka hada da Taraktocin noma, kayan Haro, kayan yin girbin amfanin gona da kuma sauran wasu kayan aikin noma.
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
- 2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC
“Muna daukar kasar nan a matsayin daya daga cikin kasashen da suka mayar da hankali wajen aikin noma a fadin duniya, domin muna fitar da ingantaccen amfanin gona zuwa kasuwannin daban-daban a duniya tare kuma da tabbatar da kowane dan Nijeriya ya samu abinci mai gina jiki,” in ji Tinubu.
“Muna tunkaho da abin da muke ci gaba da yi, domin wannan kokarin na daga cikin alkawuranmu na yakin neman zabe da muke burin cika wa al’ummar wannan kasa.”
Tinubu ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa ta dauki fannin aikin noma da matukar muhimmanci, domin fannni ne da ke samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasa.
“Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban.
Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000.
Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000.
Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa.
Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan shiri, wanda yake daidai na aikin noma a duniya, hakan zai kara bunkasa aikin noman kasar da samar da wadataccen abinci da kuma kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
“Ina so mu dauki wannan rana ta kaddamar da wannan shiri tamkar ranar farako ce da Nijeriya ta yunkuro, domin farfado da fannin aikin noman,“ in ji Tinubu.
“Yin noma da kayan aiki na zamani, shi ne kadai zai iya mayar da manoma tamkar wasu manyan jarumai,” a cewar shugaban.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, wannan shiri; an yi shi ne bisa hadaka da gwamnatin tarayya da kuma kamfanin da ke kera kayan aikin noma na zamani da aka fi sani da ‘APRE BNCC’.
Shi ma, babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa; shirin ya kara tabbatar da yunkurin gwamnatin tarayya, wajen kara habaka fannin aikin noma na kasar, wanda kuma shi ne babban ginshikin ciyar da ta tattalin arzikin kasar gaba.
“Taron na yau da ka kaddamar, ba wai kawai shiri ne don mu ba, illa kawai wata manufa ce ta gwamnatin tarayya na cimma kudurin habaka fannin aikin noman kasar,“ in ji Kyari.
“Ana sa ran za a gudanar da shirin ne, a hekt sama da 550,000 tare da kuma da samar da sama da tan miliyan biyu na hatsi, inda kuma shirin zai samar da ayyukan yi sama da 16,000, wanda kuma sama da ‘yan cirani 560,000 da ke shiyoyi shida na kasar nan, za su amfana, a cewar Ministan.”
Kazalika, Kyari ya bayyana cewa; shirin ya kuma hada da samar da ingantattun Taraktocin noma 2,000, da kayan haro da na fanfunan ban ruwa masu feshi da kayan girbi da sauran makamantansu.
“Mun tanadi sama da na’urori masu kwakwalwa guda 9,000 da kuma kayan gyaransu guda 9,000,” in ji Ministan.
Shi kuwa, a nasa jawabin a wajen taron; Mataimakin Fira Ministan Jamhuriyar Belarus, Bictor Karankebich, ya nuna jin dadinsa kan wannan yarjejeniyar da Nijeriya ta kulla da kasarsa.
Ya bayyana cewa, Jamhuriyar ta Belarus, tana da dogon tarihi wajen kera kayan aikin noma, musamman duba da cewa; kasar ta tura kayan aikin noma da ta kera zuwa sama da kasashe 100 da ke fadin duniya.
Ya ce, shirin wanda ya kasance kashi na farko; ya jaddada muhimmancin bukatar kara hada guiwa, domin wanzar da kashi na biyu na shirin a kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, kashin na wannan shiri, ya hada da samar da cibiyoyin hada Taraktocin noman da sauran kayan aikin noma da kuma bai wa manoma horo, domin sanin yadda za su sarrafa kayan aikin noman, wadanda akasarin kayan na zamani ne.
Idan za a iya tunawa, Majalisar Zartarwa ta Kasa a watan Agustan shekarar 2024 ne, ta amince da yarjejeniya a tsakanin Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci da kuma Jamhuriyar ta Belarus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp