Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce ya mika sunan abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023 ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
- 2023: Tinubu Ya Zabi Kabir Ibrahim Masari Daga Katsina A Matsayin Mataimakinsa
- Gamayyar Kungiyoyin Sun Bukaci Buhari Da APC Su Zabi Boss Mustapha A Mataimakin Tinubu
Duk da cewa dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC bai bayyana sunan abokin takarar tasa ba, ya ce ya mika wa INEC fom din takarar.
Wasu rahotanni sun tabbatar da Tinubun ya zabi Kabiru Masari dan uwan gwamnan Katsina Masari a matsayin mataimakinsa na wucin-gadi kafin hukumar zaben ta bayar da damar sauye-sauyen mataimaka gabanin zaben 2023.
Fom din ba zai cika sharuda ba, ba tare da sunan abokin takarar shugaban kasa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp