Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, matsayin Mai Ba Shi Shawara na Musamman kuma Kwamishinan Shirin Inganta Kiwo a Nijeriya.
Jega, wanda ya jagoranci Kwamitin Shirin Inganta Kiwo tare da Tinubu, zai jagoranci aiwatar da muhimman sauye-sauye, ciki har da samar da Ma’aikatar Kiwo.
- Zuwa Karshen Fabarairu Yawan Musayar Kudaden Da Aka Adana Na Sin Ya Kai Dala Tiriliyan 3.2272
- Nijeriya Ta Yi Asarar Tiriliyoyin Naira Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba – Gwamnati
Wannan naɗi na da nufin inganta kiwo da magance matsalolin da ke hana ci gabansa.
Jega mai shekaru 68 na da ƙwarewa mai zurfi a harkokin mulki da tsara manufofi, wanda zai taimaka wajen inganta fannin kiwo da tabbatar da ɗorewar sauye-sauyen da ake aiwatarwa.
Wannan mataki na gwamnatin Tinubu na nuni da yadda ta ke da niyyar bunƙasa fannin kiwo ta hanyar tsare-tsare masu ɗorewa, wanda zai taimaka wajen rage matsalolin da suka shafi noma da kiwo a ƙasar nan.
Ana sa ran shirin zai inganta samar da abinci, rage rikice-rikicen Makiyaya da Manoma, da kuma samar da damarmaki ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke dogaro da kiwo a matsayin sana’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp