Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabannin hukumomi da rassa da suke karkashin ma’aikatar yada labarai ta kasa.
Chief Ajuri Ngelale, babban mashawarcin shugaban kasa a bangaren yada labarai, shi ne ya sanar da hakan ta cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis.
- Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Zamanintar Da Kasashen Duniya Cikin Shekaru 10 Masu Zuwa
- Rashin Tsaro: Wike Zai Rufe Tashoshin Motar Da Ba Sa Kan Ka’ida A Abuja
Bayan sallamar wadanda suke kai, Tinubu ya nada sabbin shugabannin da za su maye gurbinsu nan take.
Sabbin wadanda aka nada sun hada da
(1) Hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) — darakta-janar / CEO — Mista Lanre Issa-Onilu
(2) Gidan Talebijin ta kasa mallakin Gwamnatin tarayya (NTA) — darakta-janar / CEO — Mista Salihu Abdulhamid Dembos
(3) Gidan Rediyon tarayya mallakin Gwamnatin tarayya (FRCN) — darakta-janar / CEO — Dokta Muhammed Bulama
(4) Hukumar (NBC) — darakta-janar / CEO — Mista Charles Ebuebu
(5) Gidan Rediyon muryar Nijeriya (VON) — darakta-janar / CEO — Mista. Jibrin Baba Ndace
(6) Hukumar sanya ido kan tallace-tallace ta kasa (ARCON) — darakta-janar / CEO — Dokta Lekan Fadolapo
(7) Kamfanin Dillacin Labarai ta kasa (NAN) — Manajan Gudanarwa / CEO — Mista Ali Muhammed Ali
(8) Nigerian Press Council (NPC) — babban sakararen kuma babban jami’in gudanarwa, Mista Dili Ezughah.
Tinubu ya bukaci wadanda ya nadan da su tabbatar da yin gaskiya da rikon amana a shugabannin da aka ba su kuma su kasance masu bullo da sabbin dabaru domin samar da damarmaki ga ‘yan kasa.
Kazalika, ya nemi su tabbatar da bada nasu gudunmawar wajen inganta hadin kai a tsakanin al’umma domin ci gaban kasa.
Sannan, ya kalubalance su da su yi amfani da gogewarsu da kwarewarsu domin kyautata aiki.
A cewar sanarwar dukkanin nade-naden za su fara aiki ne nan take.