Kwamitin shugaban kasa Bola Tinubu a kan sake yi wa tsarin karbar haraji kwaskwarima a kasar nan, ya bayyana cewea, a halin yana tattaunawa da gwamnanonin jihohin tarayyar Nijeriya don cimma yarjejeniyar da zai kai ga janye karbar wasu kananan haraji da ake dorawa kayan abinci da ake zirga-zirga da su tsakanin yankin arewa da kudancin Nijeriya.
Kamitin ya ce, tattaunawar zai kai ga dakatar da harajin da gwamantin jihoji da na kananan hukumomi suke yi, wanda yana takurawa masu safarar kayan abinci a tsakanin jihohin tarayyar Nijeriya.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya Gidan Dakta Idris Dutsen Tanshi
- AFCON 2023: An Fitar Da Jadawalin Zagaye Na 16
Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya bayyana haka a tattunawarsa da gidan talabijin na ‘Channels’ inda ya yi bayani a kan irin ci gaban da kwamitin ke samu a aikinsa na samar da wani tsari na musanmman ga yanayin karbar haraji a Nijeriya.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da akwamitin watanni kadan bayan ranstar da shi a kan karagar mulki, inda aka dorawa kwamitin samar da ingantacciyar tsarin da zai bunkasa yanayin karbar haraji a kasa ya kuma kai ga bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
A tattauanwar, Oyedele ya ce, irin wadanna kananan harajin basa karawa tattalin arziki komai sai dai takurawa al’umma. Ya yi korafin cewa yawancin harajin da ake dorawa kayan abinci da ke zirga-zirga da su daga kudancin zuwa arewacin kasar nan suna takurawa al’ummar Nijeriya kwarai da gaske.